Ya bukaci Shugaban kasa ya sauya alkalan kotunan zabe
dan siyasa a Jihar Kurosriba, Alhaji Muhammadu Loto ya bayyana cewa akwai bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hattara da alkalan kotunan kasar nan da ke sauraron kararrakin zabe. Ya shawarci shugaban da cewa ya kamata ko dai ya sauya su da wasu, ko kuma ya sauya masu wuraren aiki, domin kada su kawo […]
dan siyasa a Jihar Kurosriba, Alhaji Muhammadu Loto ya bayyana cewa akwai bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hattara da alkalan kotunan kasar nan da ke sauraron kararrakin zabe.
Ya shawarci shugaban da cewa ya kamata ko dai ya sauya su da wasu, ko kuma ya sauya masu wuraren aiki, domin kada su kawo masa cikas a gwamnatinsa; musamman idan aka yi la’akari da irin salon hukuncin kararrakin zabe da aka kai gaban kotunansu suke yankewa.
dan siyasar ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya.
Ya ce: “Ina ba mai girma Shugaban kasa shawara da ya kula da halayen wasu daga cikin alkalan kotunan kasar nan, masu shari’ar zabe, domin babu abin da suke yi face kwace gaskiyar mai gaskiya su bai wa mara ita.”
Ya ci gaba da cewa: “A duba yadda shari’ar zaben Gwamnan Jihar Akwa Ibom da ta Ribas ta kaya mana. An yi wa mai gaskiya kwacenta, an bai wa mara gaskiya nasara. Don haka wannan babu abin da za mu ce face yi wa demokuradiyyya da Gwamnatin Buhari zagon kasa.” In jishi.
Alhaji Loto ya ci gaba da cewa: “Kana jin irin yadda ake tafiyar da shari’a a kasar nan bai da tsari, rashin dacewar ta baci saboda ana ba mara gaskiya gaskiya, a hana wa mai ita. Domin idan ka bi diddigin abin akwai wuraren da ba a yi zabe ba ma da yawa a jihohin Akwa Ibom da Ribas amma aka ce jam’iyyar PDP ce ta ci. Ka ga wannan kin gaskiya ne. Ni dai shawarata ga Shugaban kasa ita ce, ya yi hattara da alkalan. Idan ma ta kama ya canja su ne to ya canja su, domin ma’aikatar shari’a zuciyar kasa ce. Idan ya kyale su za su iya jawo masa matsala. Abin da ni na gani na hango masa ke nan.”