Ya bukaci ’yan jarida su rika bayyana gaskiyar al’amuran da ke faruwa a Jihar Kebbi
Walin Kalgo kuma tsohon limamin sojoji Alhaji Abubakar Atiku ya bukaci ’yan jaridar da ke aiki a Jihar Kebbi, su rika bayyana gaskiyar al’amuran da suke faruwa a jihar bisa gaskiya da adalci maimakon zama sai abin da aka gaya musu. Walin Kalgon ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a […]
Walin Kalgo kuma tsohon limamin sojoji Alhaji Abubakar Atiku ya bukaci ’yan jaridar da ke aiki a Jihar Kebbi, su rika bayyana gaskiyar al’amuran da suke faruwa a jihar bisa gaskiya da adalci maimakon zama sai abin da aka gaya musu.
Walin Kalgon ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Bunza, inda ya bukaci ’yan jaridar su rika duba yadda al’ammura ke tafiya daki-daki musamman nan gaba da za a tsunduma cikin harkokin siyasa da kuma bangaren ayyukan da gwamnatin jihar ta ce ta yi, don bayyana gaskiyar al’amura.
Walin ya jawo hankalin ’yan jarida mazaunar Jihar Kebbi, cewa su zagaya makarantun jihar su ga halin da suke ciki na rashin tsabta a wuraren kwanan dalibai da wurin cin abinci da kuma rashin kwararrun malamai. Ya ce wasu makarantun abinci ba ya isar dalibai sai iyayensu sun rika aika musu da abinci.
Alhaji Abubakar Atiku ya ce gwamnatin jihar ta ce yara ba za su koma makaranta ba sai an kawo na’urar gwada cutar Ebola, amma ga shi sun koma ba ko na’urar gwada nauyi ba a kawo ba balle ta Ebola.