Ya burma wa mai juna biyu wuka a ciki

A makon da ya gabata ne wani mutum mai suna Enoma da ke unguwar Ida cikin garin Benin Jihar Edo ya daba wa wata matar aure mai juna biyu wuka a ciki. Mutumin da aka tuhuma da aikata haka, da ne ga mai gidan da mijin matar ke haya. Kamar yadda shaidun gani da ido […]

Ya burma wa mai juna biyu wuka a ciki
Ya burma wa mai juna biyu wuka a ciki

A makon da ya gabata ne wani mutum mai suna Enoma da ke unguwar Ida cikin garin Benin Jihar Edo ya daba wa wata matar aure mai juna biyu wuka a ciki. Mutumin da aka tuhuma da aikata haka, da ne ga mai gidan da mijin matar ke haya.

Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana yadda al’amarin ya faru, sun ce Enomo ya fara yin amfani da fasassun kwalabe a kan matar kafin daga bisani ya cire wata wuka ya burma mata a cikinta, duk da cewa babu wani mutum daya da ke zaune unguwar da ya fayyace ko mene ne ya hada shi da wannan matar ba.
Amma sai dai sun yi bayanin cewa bayan Enomo ya gama wannan aika-aikar sun yi kokarin ganin sun kama shi amma ya yi ta razana su da wukar da ke hannunsa. “Muka rasa ta inda za mu bullo masa, kafin daga bisani muka aika aka sanar da ’yan sanda, suka zo mana da dauki.”
Kafin zuwan ’yan sanda, an garzaya da matar zuwa Asibitin Koyarwa na Benin, domin ceto ranta da abin da taka dauke da shi. Ganin ta fara nakuda, nan take likitoci suka yi mata aiki, suka fitar da jaririn da ke cikinta kuma suka ci gaba da ba ta kulawa.
Mijin matar, Mista Ajayi da likitoci na asibitin, a bayaninsu sun ce jaririn da aka fitar babu abin da ya samu lafiyarsa, don haka mijin matar ya ce ya fi damuwa da yanayin ita mai jegon, ganin irin raunukan da ke jikinta na hujin kwalabe da na wuka.