Ya burma wa matarsa wuka a ciki
Babbar Kotun Jihar Kano da ke Gezawa ta gurfanar da wani magidanci mai suna Muhammad Tukur mai kimanin shekara 55 bisa zarginsa da laifin kashe matarsa ta hanyar burma mata wuka a ciki.dan sanda mai gabatar da kara Nura Ahmad ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin wanda mazaunin Unguwar Hotoro cikin birnin Kano […]

Babbar Kotun Jihar Kano da ke Gezawa ta gurfanar da wani magidanci mai suna Muhammad Tukur mai kimanin shekara 55 bisa zarginsa da laifin kashe matarsa ta hanyar burma mata wuka a ciki.
dan sanda mai gabatar da kara Nura Ahmad ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin wanda mazaunin Unguwar Hotoro cikin birnin Kano ne ya yi amfani da wuka inda ya farke cikin matarsa mai suna Binta Mohammad lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Ya gabatar wa kotun shaidu wadanda suka ga lokacin da lamarin ya faru. Daga cikin shaidun akwai dan wanda ake zargin mai suna Kabiru Tukur wanda ya shaida wa kotun cewa ya ji ihun matar babansa da ya fito daga daki sai ya ga mahaifinsa rike da sharbebiyar wuka ga jini na diga daga jikinta.
Haka shi ma makwabcin wanda ake zargin mai suna Yusuf Mohammad ya shaida wa kotu cewa ya shigo gidan ya iske makwabcinsa rike da wuka a hannunsa wacce ta jike da jini face-face, a gefe guda kuma ga matar a kwance cikin jini male-male.
Da aka waiwayi wanda ake zargin ya bayyana cewa ba mamaki idan har ya aikata wannan laifi, kasancewar ya dade yana fama da larurar tabin hankali.
Sai dai Alkalin Kotun Mai shari’a Muhamamd Yahya ya dage sauraran shari’ar zuwa ranar 26 ga wannan wata don ci gaba da saurarar shari’ar tare da gudanar da bincike game da gaskiyar da’awar wanda ake zargin.