Ya caka wa matarsa wuka har lahira

Ana zargin wani magidanci da soka wa matarsa wuka ya kashe ta a yankin Korinda na Karamar Hukumar Konshisha da ke Jihar Binuwai.

Ya caka wa matarsa wuka har lahira

‘Yan sanda

Ana zargin wani magidanci da soka wa matarsa wuka ya kashe ta a yankin Korinda na Karamar Hukumar Konshisha da ke Jihar Binuwai.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta shaida wa wakiliyarmu cewa ma’auratan sun samu wata takaddama ce a ranar Talata, inda a garin haka, mijin ya soka wa matar wani abu mai kaifi kamar wuka, ta ce ga garinku nan.

Dai da ce zuwa lokacin ba su da cikakken bayani, suna jiran DPO na yankin Konshisha ya turo rahotonsa domin samun karin bayani kan aihinin abin da ya faru.

Wasu mazauna yankin na Korinya sun bayyana suna marigayiyar a matsayin Mngusunun.

Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna

Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo