Ya cinna wa matarsa wuta, ya kai kansa ofishin ’yan sanda
Rahotanni sun bayyana cewar mijin ya jima yana zargin matar tana bin maza a waje.
Wani mutum ya ƙone matarsa, Misis Chioma Nwana, har lahira bayan ya zuba mata fetur a garin Abagana da ke Ƙaramar Hukumar Njikoka a Jihar Anambra.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a unguwar Eziezekwe da ke garin Abagana.
- Turkiyya ta dawo da sufurin jiragen sama zuwa Syria bayan shekara 13
- Shaguna 500 sun ƙone a gobarar kasuwar katako ta Sakkwato
Rahotanni sun bayyana cewa matar ta rasu ne da safiyar ranar Laraba a wani asibiti sakamakon munanan ƙuna da ta samu.
Mijin matar ya sha zarginta da cin amanar aurensu, wanda hakan ya janyo yawan faɗa a tsakaninsu.
A ranar da lamarin ya faru, matar ta dawo gida daga tafiya, inda mijinta ya tare ta yana zarginta da cin amanarsa da wani.
Sai ya zuba mata fetur sannan ya banka mata wuta.
Bayan aikata laifin, mijin ya miƙa kansa ofishin ’yan sanda da ke Abagana.
Wani mazaunin garin ya ce, “Mijin da ya ƙone ta, ya tafi ofishin ’yan sanda da kansa don bayar da labarin abin da ya aikata.
“Yana zargin matarsa tana neman maza a ƙauyen.”
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya ci tura, domin ba ya ɗaukar waya lokacin da aka kira shi.