Ya cinna wa yaro wuta a kan kudin wasan bidiyo
A makon da ya gabata ne wani matashi mai shekaru 19 wanda kuma ke gudanar da sana’ar kallo (Tb game) a unguwar Gwammaja cikin birnin Kano mai suna Kawu-kawu, ya kona wani abokin cinikinsa mai suna Saifullahi Jinjiri a kan rashin canji.Lamarin mai kama da almara ya faru ne da misalin karfe biyar da rabi […]

A makon da ya gabata ne wani matashi mai shekaru 19 wanda kuma ke gudanar da sana’ar kallo (Tb game) a unguwar Gwammaja cikin birnin Kano mai suna Kawu-kawu, ya kona wani abokin cinikinsa mai suna Saifullahi Jinjiri a kan rashin canji.
Lamarin mai kama da almara ya faru ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma inda Saifullahi ya gama kallo a wani gidan kallo mallakar Kawu-kawu. Bayan da Saifullahi ya gama kallo ne sai Kawu-kawu ya nemi ya biya shi Naira 50 a matsayin kudin kallon da ya yi, inda shi kuma Saifullahi ya dauko takardar Naira 200 ya mika masa da niyyar ya dauki kudinsa ya ba shi sauran canjinsa.
Sai dai hakan bai yi wa matashi Kawu-kawu dadi ba, kasancewar ba shi da canji a wurinsa, sannan kuma ya aiki kaninsa ya samo canji a wadansu wuraren amma bai samu ba. Hakan ya sa ya kara fusata nan da nan sai ya dauko jarkar fetur ya kwara a jikin Saifullahi sannan ya dauko ashana ya kyasta ya jefa masa a jiki. Nan da nan kuwa wuta ta kama cin jikinsa fal-fal inda keyarsa da wuyansa da wani sashe na bayansa da kirjinsa suka kone.
Saifullahi mai shekaru 17, wanda a yanzu haka yake kwance a gida yana jinyar mikin wutar da ya samu a dalilin wannan waki’a, ya shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru kamar haka, “ Bayan mun taso daga makarantar Islamiyya sai na canza kayan makaranta na fito na tafi gidan kallo inda ake yin Tb game. Bayan na gama sai mai gidan kallon Kawu-kawu ya ce na biya shi Naira 50 sai na ba shi takardar Naira 200. Sai ya ce ba shi da canji. A nan sai ya aiki kaninsa ya je ya samo canji, amma shi ma bai samo ba. Da aka rasa canji sai ya ce wai na raina masa hankali, me ya sa da na san ba ni da canji na zo na yi kallo. Daga nan sai ya dauko jarkar man fetur ya kwara min a jiki, kafin na yi kokarin gudu har ya kyasata ashana ya jefa min a jikina. Haka na taho da gudu ina neman taimako amma kowa ya gan ni wuta na cin jikina sai ya gudu a haka har na isa shagon wani mutum mai kanti sai na sanya hannu na debi ruwan da yake sayarwa na rika watsa wa a jikina, a haka dai wutar ta mutu, sannan na cire rigar da ke jikina.” Inji shi.
Hajiya Alga Jinjiri ita ce kakar Saifullahi Jinjiri, ta bayyana wa Aminiya yadda ta ga Saifullahi bayan an kona shi. “A lokacin da abin ya faru ina gidan wata ‘yarmu da ta haihu, sai ga wata ‘yar wan mijina mai suna Gambo ta shigo tana nemana sannan ta gaya min cewa ga shi can an zazzaga wa Saifullahi fetur an kone shi. Nan da nan na fara salati, a nan muka baro gidan haihuwa muka nufi gida. Muna isa gida sai muka tarar har sauran ‘yan uwa sun yi mota biyu sun kai shi asibiti. Ina zaune muna jajantawa sai ga shi an kawo min shi kamar gunki.” Inji ta.
‘Yan uwan Saifullahi sun bayyana cewa duk da cewa ba su yafe wannan tabargaza da aka yi musu ba, amma hakan ba zai sa su dauki doka a hannunsu ba. A cewarsu, suna nan suna jiran hukuncin da hukuma za ta yanke game da lamarin.
Aminiya ta tattauna da mutanen unguwar Gwammaja inda suka bayyana cewa sun san Kawu-kawu da bakar zuciya, domin a cewarsu, wanann ba shi ne karo na farko da yake aikata irin hakan ba, domin a wadansu lokuta a baya ya taba cire wa wani yaro kunne, haka kuma akwai yarinyar da ya taba yankan ta a cinya wai don sun samu sabani da su.
Wata kungiya mai fafutukar kare hakkin bil’adama mai suna Network for Justice ta bakin shugabanta Malam Bala Abdullahi, ta yi kira ga Sufeton ‘Yan sanda na kasa da Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano da su tabbatar an yi adalci wajen nema wa Saifullahi hakkinsa.
Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bakin kakakinta ASP Magaji Musa Majiya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa a yanzu haka wanda ake zargin yana hannunsu, da zarar kuma an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kuliya.