Ya cire hakoran yayan budurwarsa
An gurfanar da wani saurayi da abokinsa a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano bisa zarginsu da cire hakoran yayan budurwarsa.dan sanda mai gabtar da kara a kotun Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa a ranar 29 ga watan Yulin bana, wani matashi mai suna Yahaya Isyaku […]
An gurfanar da wani saurayi da abokinsa a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano bisa zarginsu da cire hakoran yayan budurwarsa.
dan sanda mai gabtar da kara a kotun Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa a ranar 29 ga watan Yulin bana, wani matashi mai suna Yahaya Isyaku Tudun Fulani ya yi karar Yusuf Abubakar ’Yar Akwa wanda saurayin kanwarsa ne da abokinsa Usman A. Usman Kundila cewa sun buga masa katako a baki lamarin da ya yi sanadiyyar zubewar hakoransa biyu.
Mai gabatar da karar ya ci gaba da shaida wa kotu cewa wadanda ake zargin sun aikata wannan danyen aiki ga yayan budurwar tasu ne a kan ya hana su nemanta, bisa hujjar cewa bai amince da dabi’un saurayin ba.
Laifuffukan da ake zargin matasan da aikatawa sun hada da hadin baki da jin rauni ga wani kuma a cewar mai gabatar da karar sun saba wa sashi na 120 da 161 da 121 na kundin shari’a da hukunce-hukuncensu.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta laifuffukan da ake zarginsu, inda Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Imam ya bayar da umarnin a tsare su a kurkuku zuwa ranar 20 ga Agustan nan don ci gaba da sauraren shari’ar.