Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700

Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya.

Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700

Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya.

Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa.

Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i

Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi.

A nan ne taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu, inda ƙanin ya zaro wuƙa ya daɓa masa, sannan ya tsere bayan ya ga ’yan banga za su kawo ɗauki.

Sanusi ya ce ’yan banga da sauran mutane ne suka kai wan nasa asibiti.

Wani ɗan banga, Bala Suleiman, ya bayyana cewa ganin su ne ya sa wanda ake zargin ya tsere.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin sanannen ɗan shaye-shaye, kuma a baya ya taɓa kai wa wasu mutum uku farmaki.

Ya ce suna ci gaba da bin sawunsa, kuma wanda aka taka wa wukar yana samun sauƙi a asibiti.

Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya

Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira

Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700

Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu