Ya dace a ba ‘yan Majalisar Tarayya kariya?
A makon jiya ne Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wani quduri da zai ba ‘yan Majalisar Dokoki ta Qasa kariya. Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin mutane da masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane kuma ga amsoshin […]
A makon jiya ne Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wani quduri da zai ba ‘yan Majalisar Dokoki ta Qasa kariya. Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin mutane da masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane kuma ga amsoshin da suke bayarwa:
Bai kamata a ba ‘yan majalisa kariya ba – Alhaji Bala Nuhu
Daga Ahmad Ali, Kafanchan
Bala Nuhu: “Ni a ra’ayina ’yan majalisa da suka haxa da na wakilai da na dattawa ba su cancanci kariya ta kowace fuska ba. Na farko ka ga su ke kusa da talakawa a matsayin wakilansu a Majalisar Tarayya waxanda suke kai buqatar yankinsu a majalisa. Duk wani kaso nasu ko na yankinsu ba a yi musu sakaci da shi amma me suke tsinanawa da shi? Na biyu shi ne mutanen nan ba sa barin Shugaban Qasa ya yi wasu muhimman abubuwa da suka dace sai su yi ta kawo cikas to ta ina irin waxannan mutane su ka cancanci kariya? Mutum nawa ne a cikinsu waxanda babu wata tuhuma a kansu? Mutum nawa ne a cikinsu waxanda ba su da matsala da jama’ar da su ka zave su? Ni a ra’ayina a matsayinsu na ’yan hana ruwa-gudu ba su kariya tamkar durqusar da dimokraxiyyarmu ce ta kowace fuska.”
Bai kamata a ba su kariya ba – Alhaji Dauda Tarai
Daga Ahmad Ali, Kafanchan
Alqasim Haruna: “Kwata-kwata bai dace a ba su kariya ba domin bai wa ’yan majalisa kariya babban haxari ne ga dimokraxiyyar Najeriya, saboda a matakan gwamnati da muke da su babu wani sashe da ke da manyan da ake tuhuma da cin hanci da rashawa irin sashin ’yan majalisa. Kalli misalin Bukola Saraki da waxansu tsofaffin gwamnonin da ke majalisa a yanzu. Ba kwanan nan (Kasafin 2016) aka samu hanun ’yan majalisa dumu-dumu kan yin cushe a cikin kasafin kuxi ba (Padding)? Ka ga ke nan bai wa irin waxannan mutane kariya tamkar ba su lasisin ci gaba da almundahana daga inda suka tsaya ne. Ni a ra’ayina ba na goyon ba su kariya saboda hakan zai yawaita cin hanci sannan zai kawo cikas ga yiwuwar yi wa talakawa aiki saboda rashin jituwa a tsakaninsu da Majalisar Zartarwa. A qarshe ina so a koma ra’ayin tsohon Shugaban Qasa Umar Musa ’Yar’aduwa da ya ba da shawarar a cire kariyar fuskantar tuhuma ga Shugaban Qasa da gwamnoni, balle a ba ’yan majalisa.
Ba wannan muke buqata ba – Abubakar Haruna
Isiyaku Muhammed
Abubakar Haruna: “Ba ma buqatar a ba ’yan majalisa wata kariya yanzu. Abin da muke buqata shi ne kowa ya yi aiki yadda ya kamata. Majalisa su yi aikinsu yadda ya kamata, su ma vangaren zantarwa su yi aiki yadda ya kamata ba wai maganar bayar da kariya ba.”
Kariya wacce? – Ahmad Abubakar Abdulmalik
Isiyaky Muhammed
Ahmad Abubakar Abdulmalik: “Wace irin kariya kuma? Ai dama kamar suna qarqashin wata iri kariya ce da suka qulla a tsakaninsu. Yanzu idan kuma aka qara musu kariya, to zai zama sun qara samun qarfin da zu ci gaba da yin abin da suka gadama a majilisa. Amma kuma duk da haka ina so majalisa ta zama tana da qarfi domin kada ta zama ’yar amshin shata.”
Bai dace ba – Abdullahi Alkwatanawi
Daga Abbas Ɗalibi, Abekuta
Abdullahi Alkwatanawi: “Bai dace a ba su kariya ba saboda su wakilan al’umma ne, muddin aka ba su kariya an ce su yi abin da suka gadama ke nan, don haka a ra’ayina bai dace a ba su kariya ba.”