Ya dace a bar fursunoni su rika kada kuri’a a lokacin zabe?
A kwanakin baya ne wata kotu ta yanke hukuncin ba fursunoni damar kada kuri’a a lokacin zabe. Hakan ya jawo muhawara a tsakanin mutane, inda wadansu suke ganin cewa bai kamata a bar masu laifi su rika yin zabe ba, wadansu kuma na ganin ai su ma ’yan kasa ne kuma suna da ’yanci kamar […]
A kwanakin baya ne wata kotu ta yanke hukuncin ba fursunoni damar kada kuri’a a lokacin zabe. Hakan ya jawo muhawara a tsakanin mutane, inda wadansu suke ganin cewa bai kamata a bar masu laifi su rika yin zabe ba, wadansu kuma na ganin ai su ma ’yan kasa ne kuma suna da ’yanci kamar kowa. Domin jin ra’yoyin mutane a kan wannan batu, wakilan Aminiya sun zagaya kuma ga abin da mutane suka fada:
Ya da ce su yi zabe – Kwamared Mukhtar
Daga Muhammed Yaba, Kaduna
Kwamared Muktar Muhammed: “Hakkinsu ne su yi zabe kamar kowane dan Najeriya domin kuwa laifin da suka yi har aka tsare su bai kamata ya hana su zaben wanda suke son ya shugabance su ba. Hakan ya sa nake ganin ba laifi ba ne a bari su yi zabe kamar kowa.”
Bai kamata ba –Malam Abubakar
Daga Abbas Dalibi, Legas
Malam Abubakar Alassan Usman: “A gaskiya ni a ra’ayina duk wanda da yake gidan kaso bai kamata ya yi zabe ba, saboda har yanzu hukumar zabe tana fama da matsaloli kamar na canjin wurin zabe. Kamar wanda ya bar Legas ya koma Kano da ’yan Najeriya mazaunan kasar waje ba sa zabe saboda hukumar zaben ba ta da wadatar zartar da ko kuma gudanar da zaben da ya shafe su ballantana wadanda suke gidan kaso da ake canja musu mazauni daga wannan gidan kaso zuwa wancan.”
Ya dace fursunoni su yi zabe –Fatima Paga
Rabilu Abubakar, Gombe
Hajiya Fatima Muhammad Paga: “Dan fursuna na da ’yancin yin zabe domin babu dokar da ta hana shi yin zabe. Zai yiwu a lokacin da dan fursuna yake zaman kaso ana yin rajistar zabe, idan ba a ba shi dama ya yi ba har aka gama idan ya fito ba dama ya yi zabe don bai da riaista hakan ta sa an yi asarar kuri’arsa ke nan. Ko ba za a ba su dama su fito waje ba, a kai musu akwatin zabe gidan fursunan su zabi wanda suke so don su ma ’yan kasa ne masu ’yanci kuma babu dokar da ta ce don mutum yana gidan kaso ba zai yi zabe ba, kuma da yawa wadanda suke zaman kaso jiran shari’a suke yi.”
Babu dokar da ta hana su zabe – Barista Mohammed
Daga Mohammed Yaba, Kaduna
Barister Mohammed Bello Umar: “Babu dokar da ta hana fursunoni yin zabe domin ’yancinsu ne a matsayinsu na ’yan kasa a bari su yi zabe. Kuma ai kwanan nan kotu ta yanke hukuncin cewa a bar wadanda ke tsare su rika yin zabe domin su ma ’yan kasa ne kuma babu dokar kasa da ta hana musu wannan ’yanci nasu.”
Wanda aka daure yana da tawaya da dama – Idris Danlami
Daga Abbas Dalibi, a Legas
Malam Idris Danlami Alhasan: “Ni a nawa ra’ayin wannan abu ne da ya shafi shari’a ko tsarin dokar kasa, don haka kamata ya yi a duba a gani shin me dokar kasa ko tsarin mulkin kasa ya ce game da hakan? Idan doka ta bai wa daurarru ’yancin yin zabe sai a ba su dama, idan kuma akansin haka ne ai ka ga shi ke na babu damuwa domin ai shi wanda doka ta daure yana da tawaya da dama ba wai maganar kada kuri’a kawai ba.”
Doka ba ta hana dan fursuna yin zabe ba –Ibrahim Arab
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Ibrahim Sa’idu Arab: “Shawarata ita ce a ba wa dan fursuna damar yin zabe don doka ba ta hana ba. Dan fursuna dan kasa ne kamar kowa mai cikakken ’yanci, don haka ya dace a bar shi ya yi zabe domin a kasar nan akwai dan takarar da yana gidan fursuna ya ci zaben sanata. Shiga fursuna ba ya nuna laifi, sai kotu ta tabbatar sannan ya zama mai laifi kuma don mutum yana da laifi ba zai sa a ce ba zai yi zabe ba. Don haka dan fursuna zai iya zabe.”