Ya dace a canja jadawalin zabe a fara da na ‘yan majalisu?
Fara zaben ‘yan majalisa shi ne adalci – Isah Abdullahi Hussaini Isah, Jos Isah Abdullahi; ‘’Gaskiyar magana idan ana son a yi wa al’ummar Najeriya adalci, a fara zaben ’yan majalisa maimakon a fara da zaben Shugaban kasa. Domin kowa ya ga abin da ya faru a zaben da aka yi a baya, inda jama’ar […]
Fara zaben ‘yan majalisa shi ne adalci – Isah Abdullahi
Hussaini Isah, Jos
Isah Abdullahi; ‘’Gaskiyar magana idan ana son a yi wa al’ummar Najeriya adalci, a fara zaben ’yan majalisa maimakon a fara da zaben Shugaban kasa. Domin kowa ya ga abin da ya faru a zaben da aka yi a baya, inda jama’ar Najeriya suka yi zaben sak. Wanda shi kansa Shugaban kasa Buhari yana shan wahalar wannan zabe na sak da aka yi a baya. Don haka a fara zaben ’yan majalisa shi ne daidai maimakon fara zaben Shugaban kasa. Yanzu ba jam’iyya za a zaba ba, mutum ne za a zaba. Jama’a za su zabi wanda suka ga ya dace ne. Amma idan aka ce an fara da zaben Shugaban kasa, za a kara yin irin abin da aka yi a baya. Ta yadda kowane irin mutum da wanda ya cancanta da wanda bai cancanta zai ci zaben.’’
Ya kamata a fara zaben ‘yan majalisa – Manu Isah
Hussaini Isah, Jos
Manu Isah Idris; ‘’Gaskiya abin da nake ganin ya kamata shi ne a fara zaben ’yan majalisa maimakon a fara da zaben Shugaban kasa. Saboda shi Shugaban kasa duk lokacin da aka yi zabensa musamman ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari kusan hankalin talakawa baki daya yana kansa, don haka zai iya cin zaben. Don haka ni a ra’ayina a fara da zaben ’yan majalisa maimakon a fara da zaben Shugaban kasa. Domin yin zaben ’yan majalisa da farko zai ba da dama a zabi mutanen da suka cancanta.”
Bai dace ba – Ramlat Salihu Dawaki
Isiyaku Muhammed
Ramlat Salihu Dawaki: “Bai dace a canja jadawalin zabe ba ta hanyar farawa da na ’yan majalisa sannan na gwamnoni da ’yan majalisar jihohi kafin na Shugaban kasa a karshe. Yin hakan yana nuni da rashin amfani ko watsi da dokokin zabe wadanda aka gina bisa doka da tsarin mulki na 1999. Saboda haka bin ra’ayin wasu tsirari cikin al’umma ka iya jawo rabuwar kai da haddasa rashin zaman lafiya a zaben da ke gabatowa na 2019 kawai don biyan bukatunsu suke so a canja jadawalin zaben. Idan aka canja jadawalin sai aka samu wata matsala da ba a fata sanadin bin kudurinsu, su wane ne abin zai shafa? Tunda ba tun yau ba Kotun koli ta tabbatar da ikon da Hukumar INEC ke da shi na shirya zabe, ya kamata hukumar ta tsaya tsayin daka ta ki amincewa da canja jadawalin.”
Gaskiya ya dace – Muhammadu Sabi’u
Isiyaku Muhammed
Muhammadu Sabi’u: “Dalili kuwa shi ne: yin hakan zai takaita yunkurin murde sakamakon zabe. Abin nufi: gwamnanoni da Shugaban kasa sun fi ’yan majalisa karfin iko da mulki. Ke nan idan aka fara nasu, akwai yiwuwar su yi murdiya ta hanyar juya sakamakon zaben ko kuma karkatar da nasara zuwa ga wanda ransu yake so koda kuwa ba su ne suka samu nasara ba. Idan kuma aka fara na gwamnanonin, za su samu kwanciyar hankali domin sun gama nasu yakin; za kuma su shiga na ’yan kare muradunsu (watakila cikin ’yan kare muradun nasu akwai masu takarar zama ’yan majalisa). Bugu da kari, ba za su mayar da hankali kan zaben ’yan majalisa ba in har su (gwamnonin) ba su san makomarsu ba domin ba a riga an yi nasu ba. Yin hakan kuma zai iya janyo hargitsi da tashin hankalin da watakila zai iya kawo hasarar rayuka. Abu mafi dacewa shi ne: a fara na ’yan majalisa ta yadda gwamnoni ba za su kwallafa ransu a kai ba.”
Ba zai yiwu ba – Bello Yunus
Isiyaku Muhammed
Bello Yunus: “Ai wannan canjin ba zai yiwu ba matukar ba INEC ba ce ta canja jadawalin da kanta. Wai don ’yan majalisa sun canja jadawalin zabe, bai kamata ma a rika maganar ba saboda ba su da ikon yin haka. Amma kuma ko da suna da ikon yin canjin, ni a ra’ayina suna so a fara da zabensu ne domin su samu goyon baya, kuma yanzu kan mage ya waye.”
A ci gaba da yadda jadawalin yake a da – Nusaiba M. Suleiman
Isiyaku Muhammed
Nusaiba M. Suleiman: “A ra’ayina zan so a fara da zaben Shugaban kasa domin shi ne kowa ke jira. Kuma koda an samu matsala duk da cewa ba a fata, an riga an zabi Shugaba, sauran ko daga baya sai a yi. Amma wannan tsarin ba ba daidai ba ne. Ni ba ni ma da niyyar zuwa sauran zabubbukkan idan ba na Shugaban kasa ba. Don haka gara a fara da na shi, ko kuma a ci gaba da yadda ake yi a da kawai.”