Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]

Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:

Bai kamata a mayar da su karkashin jihohi ba – Aina Lorence

Aina Lorence: “Gaskiya ni ban goyi bayan a mayar da kananan hukumomi karkashin jihohi ba, gwamma su ci gaba da cin gashin kansu, domin hakan ita ce demokuradiyya. Saboda da farko, idan ana so gwamnati ta ci gaba da zama kusa da jama’a, to wajibi ne kananan hukumomi su ci gaba da zama masu cikakken ’yanci. Misali, a nan Jihar Legas yanzu da gwamnatin jihar ta mayar da kwasar shara karkashinta, mutane suna biyan kudi da yawa, sabanin lokacin da yake karkashin kananan hukumomi.