Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 1
kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]
kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:
Bai dace a cire kananan hukumomi ba – Prince Idowu
Prince Idowu Olowu: “Muddin ana son demokuradiyya ta kankama, to wajibi ne a ci gaba da tsarin da ake da shi, inda Gwamnatin Tarayya, jihohi da kananan hukumomi kowa ke cin gashin kansa. Idan an ce a mayar da kananan hukumomi karkashin jihohi, aikin zai yi wa gwamnatin jihohi yawa kuma kar ka manta cewa yadda aka zabi gwamna haka ake zaben ciyamomi, to kaddara gwamna da wasu kananan hukumomin ba su karkashin jam’iyya guda, ke nan wadannan kananan hukumomin za su sha wahala. Haka wasu ayyuka ba za su yi saurin kaiwa ga wasu kananan hukumomin ba, domin gwamnatin jiha na da wuraren da ke karkashin kulawarta kai tsaye.