Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 2

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]

Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 2
Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 2

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:

A bar kananan hukumomi yadda suke yanzu -Aminu AbdullahiShu’aibu

Aminu Abdullahi Gusau: “Ni a ra’ayina shi ne, bai dace a cire kananan hukumomi ba daga Kundin Tsarin Mulki saboda su kansu gwamnoni ba don Allah suke ba, kuma ana cewa kananan hukumomi su ne wadanda dukiyar jama’a ke hannunsu. Amma gwamnoni sun fi su nesa da talakawa, don su babu mai ganinsu balle ya jingina da su, kullum suna kasar waje. Kafin wani shugaban karamar hukuma  ya fita waje, ai sai ka ga gwamna ya fita sau saba’in amma ciyaman bai fita sau daya ba , kuma da su ne ake hada baki ana kashe mu, kuma suna kwashe mana dukiya amma ciyaman kullum sai ka ji an ce ya biya kudin rago ko na rashin asibiti  ko kuma na likkafani.”