Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 3

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]

Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 3
Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 3

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:

Ya dace a cire su daga tsarin mulki – Mika’ilu Gusau

Malam Mika’ilu Gusau: “Ni a ra’ayina, ya dace a cire su saboda ai da su da gwamnoni danjuma ne da danjummai saboda daman yanzu ba zabe ake ba nadi ne, don haka shi shugaban karamar hukuma ba shi da katabus don dora shi aka yi. Duk abin da ya zo sai dai a ba shi abin da ake so a ba shi. Ana amfani da su ne don a ci zabe, ba domin a yi wa jama’a aiki ba. Su ma sun zama lalatattu, ba su tausayin wani talaka, don haka gara a maida su karkashin jihohi su ida kashe mutane, don babu wanda ya san inda kudaden kananan hukumomi suke a yanzu, shi ya sa ma suke taba kudin alhazai babu wani tausayi, don haka gara a koma karkashin jihohi kawai.”