Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 4
kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]
kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:
A maida su karkashin jihohi – Haruna Mai Agogo
Alhaji Haruna Mai Agogo: “Idan da gaske ake yi kuma a yi adalci kamar irin salon da Gwamnan Jihar Kano ya fara dauka, wajen rike kudade mallakar kananan hukumomi domin yin wasu ayyukan ci gaban al’umma baki daya a jihar, wannan ba laifi; na amince a mayar da kananan hukumomi a karkashin gwamnatocin jihohi. Amma, idan har ba za a kwatanta gaskiya da yin adalci ba, to, a kyale kananan hukumomi su ci gaba da zama a irin halin da suke ciki a yanzu. Kowane aka yi yana da kyau, idan har za a yi aiki ne tsakani da Allah.”