Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 5

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin […]

Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 5
Ya dace a cire tsarin kananan hukumomi daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 5

kananan hukumomi na daya daga cikin tubala uku na matakan gwamnati a Najeriya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tabbatar. Sai dai a yau jihohi sun dabaibaye su, sun hana su rawar gaban hantsi. A yanzu wasu ma na ganin cewa ya kamata a cire tsarinsu na cin gashin kai, a mayar da su karkashin jihohi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a cire su ko kuwa a bar su yadda suke a yanzu? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga jama’a:
Bai kamata a cire su ba – Babangida ’Yankara

Alhaji Babangida ’Yankara: “Bai kamata a mayar da kananan hukumomi a karkashin gwamnatocin jihohi ba. Kamata ya yi a kara musu karfin gwiwa kuma a kyale su su ci gashin kansu. A wasu lokuta za ka ga shugaban karamar hukuma yana neman rancen ’yan kudi daga wani attajiri domin hidimar karbar baki da makamantansu, to, idan aka kuskura aka mayar da kananan hukumomi a karkashin gwamnatocin jihohi, an kara durkusar da su ke nan kuma an sake kirkirar hanyoyin fatara da talauci su yadu a tsakanin matasa. Rashin sakar wa kananan hukumomi mara, shi ne yake haifar da koma bayan ayyukan ci gaba a yankunansu. Muddin aka mayar da kananan hukumomi a karkashin gwamnatoci, an bullo da hanyar kara musguna wa jama’a ke nan.”