Ya dace a dage ranakun gudanar da zabukan bana?

A ranakun 14 da 28 ga watan nan na Fabrairu ne aka shirya gudanar da zabubbukan kasa. Sai dai kuma a yayin da ranakun ke gabatowa, wasu mutane na ganin cewa ya kamata a dage ranakun zuwa nan gaba, kamar yadda wasu kuma ke ganin bai dace a daga ba. Abin tambaya a nan shi […]

Ya dace a dage ranakun gudanar da zabukan bana?
Ya dace a dage ranakun gudanar da zabukan bana?

A ranakun 14 da 28 ga watan nan na Fabrairu ne aka shirya gudanar da zabubbukan kasa. Sai dai kuma a yayin da ranakun ke gabatowa, wasu mutane na ganin cewa ya kamata a dage ranakun zuwa nan gaba, kamar yadda wasu kuma ke ganin bai dace a daga ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a dage ko kuwa a gudanar da su yadda aka tsara?

Bai dace a dage zaben ba – Bala Muhammad

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Bala Muhammad Suleja: “Ba na goyon bayan dage wannan zaben. Dalili kuwa, babu wata hujjar da za ta haifar da haka. Idan za ka yi la’akari da wadanda suke wannan kiran, mutanen Jam’iyyar PDP ne. Ga alamu sun hango alamun rashin samun nasara, muddin Hukumar Zabe Ta kasa ta gudanar da wannan zaben bisa yadda ta tsara. Kar mu manta, Hukumar Zaben ta tabbatar wa jama’a cewa ta shirya domin sauke nauyin da aka dora mata. Tun da ba ita ta koka ba, ya ya za mu goyi bayan wannan matakin. Ga alamu ke nan akwai makarkashiyar da ake neman kullawa.”

Ban amince da dage zabe ba – Idris Ibrahim

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna
Idris Ibrahim Suleja: “Ban yarda a dage zaben da Hukumar Zabe Ta kasa ta yi niyyar gudanarwa daga ranar 14 ga wannan watan ba. dage wannan zaben ba shi da wani amfani, zai haifar da fitintinu a kasa. Jama’a sun gaji da gwamnati mai ci, shi ya sa suke so su canza shugabanni. Wadanda ke kai sun ki cika alkawuran da suka yi wa jama’a a baya. Misali, shekaru 16 ke nan kasar nan ke fama da karancin wutar lantarki, ga rashin aikin yi da tabarbarewar tsaro, musamman a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Uwa uba, yunwa ta zama hantsi leka gidan kowa, babu magunguna a asibitoci, likitoci da malaman jinya suna yajin aiki. Haka lamarin yake a fannin shari’a, kar ma mu yi maganar manoma wadanda ba su samun takin zamani.”

dage zaben zai kawo matsala – Umar Galadima

Abubakar Haruna, a Legas

Umar Galadima: “Bai kamata a dage zabe ba, kamata ya yi a yi shi kamar yadda aka sanya. dage zaben ba shi da amfani don zai iya kawo rikici da rudu a kasa baki daya. Shi ya sa nake kira ga hukumar zabe ta gudanar da zaben kamar yadda ta sanya ba tare wata fargaba ba.”

Bai kamata a dage shi ba  – Jibrin Musa

Abubakar Haruna, a Legas

Jibrin Musa Zaburan: “Gaskiya bai kamata a dage zabe ba domin muna son a yi zaben don mutane sun zaku a samu canji a kasar nan kuma ni ina ganin ba wani abu ba ne ya sa suke son a dage zaben ba saboda sun ga ba za su samu nasara ba, shi ya sa suka kawo maganar cewa a dage zabe saboda a samu rudu a kasa.”

Ba mu kaunar dage zabe – Maman Amina

Hamza Aliyu, a Bauchi

Maman Amina Mai Tuwo: “Kowa ya san cewa da yawa daga cikin ’yan Najeriya suna Allah-Allah a gudanar da wannan zabe domin mun gaji da wannan gwamnati wacce ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Don haka bama kaunar a dage lokacin gudanar da wannan zabe wanda za a gudanar nan da makonni biyu masu zuwa. Kuma ni yanzu haka na ajiye katin zabena a cikin akwati, ina jiran ranar zabe. Kuma ya kamata a gane cewa dukkan wadanda suke cewa a dage zaben mutane ne ’yan tsiraru, marasa kishin kasa.
“Za mu kasa mu tsare masu shirin magudi, wannan karon ba za su yi nasara ba domin yanzu kan mage ya waye. An yi magudi a shekarun baya amma zaben bana babu magudi babu satar akwati saboda haka ina kira da babbar murya ga Hukumar Zabe, kada ta dage wannan zabe.”

Bai dace a dage zaben ba- Shehu Kawule

Hamza Aliyu, a Bauchi

Shehu Kawule Gamawa: “Magana ta gaskiya ita ce, bai kamata a dage lokacin wannan zabe ba. Dalilina shi ne, idan aka dage zaben zai haifar da rudani a tsakanin ’yan Najeriya. Kowa ya san cewa zabukan da aka gudanar a 2011, an tafka magudi saboda haka zai yi matukar wahala a yi magudi a wannan zabe; domin kashi 95 cikin 100 na ’yan Najeriya sun gaji da wannan gwamnati, wacce ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Don haka kada a kuskura a dage lokacin wannan zaben kuma ya kamata masu shirye-shiryen magudi su shafa wa kansu ruwa. Abubuwan da aka aikata a shekarun baya, zai yi wahala a maimaita a wannan zabe, domin kusan kowa yana bukatar canji a siyasar Najeriya. Muna fatar Allah Ya kawo mana karshen matsalolin siyasar kasan nan.”