Ya dace a kafa dokar kashe wanda ya haddasa kashe-kashe ta soshiyal mediya?

Majalisar Dattawa tana muhawara kan wani kudirin doka da yake neman a rika kashe duk wanda ya  sanya kalaman tunzurawa a kafafen sadarwar zamani da ake kira soshiyal mediya da suka jawo kashe-kashen jama’a. Yanzu haka kudirin ya samu shigewa a karatun farko da na biyu a gaban majalisar. Ganin yadda wannan lamari ke jawo […]

Ya dace a kafa dokar kashe wanda ya haddasa kashe-kashe ta soshiyal mediya?

Ahmed Mohammed

Majalisar Dattawa tana muhawara kan wani kudirin doka da yake neman a rika kashe duk wanda ya  sanya kalaman tunzurawa a kafafen sadarwar zamani da ake kira soshiyal mediya da suka jawo kashe-kashen jama’a. Yanzu haka kudirin ya samu shigewa a karatun farko da na biyu a gaban majalisar. Ganin yadda wannan lamari ke jawo cece-ku-ce a tsakanin jama’a, wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a a kan wannan lamari:

Gaskiya ba na goyon bayan haka – Dokta Umar Mohammed

Daga Adam Umar, Abuja

A gaskiya ba na goyon kafa wannan dokar saboda ’yan siyasa da sauran masu rike da iko na iya amfani da ita a kan abokansu na hamayya. Sannan a wani bangaren kuma a hana al’umma damar fadin albarkacin baki wanda tsarin dimokuradiyya ke tutiya da shi.

Ina goyon bayan kafa wannan doka – Malam Sulaiman Hamza

Daga Adam Umar, Abuja

A gaskiya na goyi bayan kafa wannan dokar, bisa la’akari da yadda wadansu ke yada bayanin tashin hankali ta waya. Cikin kankanen lokaci sai ka ji an tare hanya ana ta kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba kan wannan labarin da wani ya yada. Wannan ba karamar musifa ba ce, kuma Allah da kanSa Ya yi horo da a guje shi.

Hukuncin bai dace ba -Madugu Chanchangi

Daga Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna

Dokar ba ta dace ba kasancewar akwai wadanda ke aikata manyan laifuffuka kamar ’yan fashi da masu garkuwa da mutane da ya kamata a yanke wa irin wannan hukunci mai tsanani. Amma ba a yi ba sai wadanda ke amfani da Intanet saboda kurum gwamnati ba ta son adawa.

Hukuncin kisa bai dace ba – Ahmed Mohammed

Daga Magaji Isa, Jalingo

Hukuncin kisa kan maganar yada kalaman kiyayaya bai dace ba. Abin da kamata shi ne a daure duk wanda aka samu da irin wannan laifi na tsawon lokaci a gidan yari. Hakan zai magance yawan fititnun da suke faruwa a dalilin maganganun nuna kiyayaya.

A mayar daurin rai-da-rai  –Aliyu Muhammad

Daga Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna

Ni ba na goyon bayan hukuncin kisa a kan wanda ya yada irin wannan labari na batanci a Intanet. Abin da kawai nake ganin ya dace majalisa ta yi shi ne ta zartar da dauren rai-da-rai akan irin wayannan mutune ba kisa ba.

Hukuncin ya yi tsauri – Muhammed Sani Aliyu

Daga Magaji Isa Jalingo

Hukuncin kisa ya yi tsauri sosai, abin da ya kamata shi a daure wanda ya yada irin wannan labari na tsawon lokaci don yin hakan zai zama manuniya ga masu irin wannan dabi’a. Kuma haka din zai magance yawan tashin hankali da kashe-kashe wadanda kalaman nuna kiyayya ke haifarwa.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara