Ya dace a rika biyan kudin fansa don karbo ‘yan makarantar da ake sacewa?
Kwanakin baya ne wadanda ake zargi ‘yan Boko Haram ne suka sace ‘yan mata a makarantar Sakandaren Dapchi da ke Jihar Yobe. Kuma a makon jiya suka dawo da su. Kasancewar an ce Gwamnatin Tarayya ta biya kudin fansa domin karbo ‘yan matan Chibok da aka sace lokacin mulkin Jonathan, kuma akwai rade-radin na Dapchi […]
Kwanakin baya ne wadanda ake zargi ‘yan Boko Haram ne suka sace ‘yan mata a makarantar Sakandaren Dapchi da ke Jihar Yobe. Kuma a makon jiya suka dawo da su. Kasancewar an ce Gwamnatin Tarayya ta biya kudin fansa domin karbo ‘yan matan Chibok da aka sace lokacin mulkin Jonathan, kuma akwai rade-radin na Dapchi ma an biya, wakilan Aminiya suka zagaya don jin ra’ayoyin mutane kan ko ya dace a rika biyan kudin fansa domin karbo daliban da aka sace?
Bai dace a biya ba – Ya’u batagarawa
Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina
Malam Ya’u batagarawa: “Abin da ya sa nace kada a biya shi ne biyan da aka yi na ’yan matan Chibok shi ya sa har wadannan su ma suka sace ’yan makarantar Dapchi. Idan aka ci gaba da biyan kudaden fansa, to babu ranar kawo karshen haka, domin za a ci gaba da samun bangarori na yin haka. Ga misali nan ga masu sacewa tare da yin garkuwa da mutane, kullum abin sai karuwa yake yi. Sannan in ana ba su kudin fansar zai sa su ci gaba da sayen makamai domin ci gaba da tayar da fitintinu a cikin kasa. Illa dai gwamnati ta lalubo wata hanyar amma ba wannan ba.”
Idan ana ba da kudi ba za su daina ba – Abubakar Bapetel
Daga Amina Abdullahi, Yola
Alhaji Abubakar Bapetel: “Idan ana ba da kudi kullum domin a fanshi yara, a ganinmu wannan abu ba za a daina ba. Kuma zai zama musu sana’a wadda a kullum sai sun saci yara su ajiye domin sannin za a ba da kudi a fansa.
Bayan ikon Allah sai ikon gwamnati domin gwamnati na iya abin da ta ga dama game da Najeriya amma yaya za a yi a ce kungiya ce za ta zo ta rika yin irin wannan abin. A ganinmu bai kamata a rika daukar kudi ana ba su fansa ba. Ya kamata gwamnati ta yi ruwa-da-tsaki don kubutar da yaran da ake sacewa ko da karfin yaki tunda gwamnati ce. Amma in har za a rika sanya kudi ana fansa abin ba zai yi dadi ba.”
Ya dace a biya ko nawa ne a karbo su – Halima Baba Ahmad
Daga Ahmed Mohammed, Bauchi
Halima Baba Ahmad: “Muddin gwamnati ta ga cewa a biya kudin fansa a karbo wadanda aka sace shi ne kawai maslaha da hanyar da za a dawo da su gida lafiya, ya kamata a biya, saboda suna tare da mutane ne da ba su sonsu ba. Duk halin da suke ciki su da iyayensu da al’ummar kasar nan ba mu da kwanciyar hankali har sai an karbo su. Wannan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga su wadanda aka sacen da iyayensu.”
Bai dace ba a ra’ayina – Abubakar A-Gyarota
Daga Amina Abdullahi, Yola
Alhaji Abubakar A-Gyarota: “A ra’ayina bai dace gwamnati ta ba da kudi ba domin tana da hanyoyi da hikimar yadda za ta koyar da sojojinta wajen kwato wadannan ’yan mata. Idan aka ce za a rika ba su kudi, hakan zai sa su ci gaba da yi. Ya kamata tun lokacin da aka fadi cewa an sace su, gwamnati ta dauki matakin da a cikin awanni biyu za a ceto su. In ana so a kamanta gaskiya, gwamnati ta koyar da jami’an tsaronta domin ganin duk yadda za su yi a gano ’yan matan.
A matsayina na dan kasa, ra’ayina shi ne, gwamnati ta rika kokarin kwato wadanda aka sace. Amma idan ta ce za ta yi amfani da kudi, wannan ya nuna ke nan gwamnati ta kasa. Tunda dai makarantun nan na gwamnati ne ba na kudi ba.”
Bai dace a biya kudin fansa ba – Tijjani Kolo
Ahmed Mohammed, Bauchi
Tijjani Kolo: “Gaskiya bai kamata a biya kudin fansa ba duk da cewa da zafi sosai ga su yaran da aka sacen da iyayensu. Dukanmu ’yan Najeriya muna jin zafin lamarin, , amma ba na goyon a rika bayan biyan kudin fansa don yin haka yana kara wa masu laifi kudi a hannunsu, kudin kuma masu nauyi, wadanda za su iya amfani da su wajen samun wadanda za su goyi bayansu bisa la’akari da yadda fatara da yunwa suka gallabi jama’a domin wanda ruwa ya ci in ka mika masa tsinin takobi sai ya kama.”
Ba na goyo bayan biyan fansa – Sidi Nasir
Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina
Mohammad Sidi Nasir: “Dalilin da ya sa ba na goyon bayan biyan fansar shi ne: Gwamnati na da masaniyar duk abin da ke faruwa, domin marigayi Janar Sani Abacha ya taba cewa babu abin da za a yi a cikin kasa har a yi awa 24 a ce gwamnati ba ta san da shi ba. Saboda haka, su ajiye maganar siyasa. Ni ina kallon abin a matsayin shirin fim kawai, domin an ce da mota da kayan sojoji ake zuwa a dauke su. Don haka babu wani biyan kudin fansa.”