Ya dace a rika gwada kwakwalwar ma’aurata kafin su yi aure?

A ‘yan kwanakin nan, an samu labarai marasa dadi, inda ake zargin wasu mata guda biyu da daba wa mazajensu kwalba ko wuka, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwa daya, yayin da dayan kuma ya ji rauni, duk da cewa Allah Ya sa da sauran rayuwarsa a gaba. sannan kuma aka yanke wa wata matar […]

Ya dace a rika gwada kwakwalwar ma’aurata kafin su yi aure?

A ‘yan kwanakin nan, an samu labarai marasa dadi, inda ake zargin wasu mata guda biyu da daba wa mazajensu kwalba ko wuka, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwa daya, yayin da dayan kuma ya ji rauni, duk da cewa Allah Ya sa da sauran rayuwarsa a gaba. sannan kuma aka yanke wa wata matar hukuncin zaman gidan kaso na shekara shida saboda kasha mijinta. Kuma an sha samun inda mazajen ke cutar da matan, har su ji mu raunuka. An dade ana irin wannan rigingimu, kuma kullum abin na kara kamari ne. Wannan ya sa wasu suke ganin kamar ba lafiya ba, domin hakanan wadanda suka yi auren so da kauna, bai kamata ace su kashe kansu ba. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan ko da dace a rika gwada kwakwalwa kafin ayi sure, kuma ga amsohin da suke bayarwa:

 

Gaskiya ya kamata – Zainab Abubakar Daga Zainab Mukhtar

Zainab Abubakar: “Gaskiya ya kamata. Na yadda cewa wasu matsalolin da ke jikin dan Adam na daukan lokaci kafin su nuna kansu, hakan ke sa mutum mai matsalar kwakwalwa ba a ganewa sai daga baya ko kuma idan wani abu ya tabo shi. Matasa da dama yanzu suna shan shisha hade da miyagun sinadarai masu sa maye, wiwi da sauransu. Saboda haka banda HIb, blood group da sauransu da ake yi kafin aure, ya kamata a hada da duba kwakwalwa. Koda ace wadanda za su yi auren suna da tabbacin ba su taba shan kayan maye ba, ya kamata su je su yi domin tsaro, Kuma banda kayan maye, akwai abubuwa da dama da suke iya jawo hauka. Matsala wajen haihuwa ko lokacin da ake dauke da juna biyu,cin mutuncin yara da sauransu na iya jawo tabin hankalin dana Adam. Mutum na iya yin rayuwa ba tare da angane, ko shi kansa ya san yana da matsalar ba har sai wani mummunan al’amari, tashin hankali ko tsananin damuwa ya sameshi sai ka ga yana wasu irin dabi’u na daban, wato ciwon ya tashi. Hakan ne ya sa ya kamata a rika gwajin kwakwalwa kafin ayi aure. Tunda dai abubuwa iri iri na faruwa a rayuwar aure.”

 

 

Ya dace tun da abin ya zama shirme –Hajiya Talatu Muhammad

Daga Abbas Ɗalibi, a Legas

Hajjiya Talatu Muhammad: “Ya dace a auna kwakwalwar tunda abin ya zo da shirme, menene shirme a nan? Kunyi aure ina so kana so, sai kuma mace ta kashe mijin don kada ya yi mata kishiya, ko arzikinsa ya habbaka wata ma taci.  Ai wannan ya zama shirme da shashanci da cin mutumcin mata wadanda ba sayi da kuma cin mutumcin addinin mu. Don haka ya kamata maza  idan za su yi aure su yi bincike, su kuma mata su sani wani harkar aiki ko kasuwanci na iya hada mazajensu da mata, sannan kuma a ina matan yanzu suka gano cewa namiji ba zai kara aure ba? Ai shi namiji yana da ikon auren mace 4, ina ganin hukuma ce bata hukunta irin wadannan mata kamar yadda ya kamata, da za a yi wa macen da ta kashe mijinta hukuncin da ya yi daidai da laifin ta da gobe wata ba za ta sake ba, don haka hakkin hukuma ne daukar  mataki don magance haka.”

 

 

Babu bukata – Alhaji Ali Alhassan

Daga Abbas dalibi, a Legas

Alhaji Ali Alhasan Madobi: “Tsakani da Allah duk inda ake neman aure babu bukatar gwajin kwakwalwarka ko ta matar da za ka aura, domin idan kana da alaka da hauka ko ita matar ne ake bukatar yin bincike kafin a kai ga aure domin ita hauka a tsarin musulumci ana gadon ta, daman kuma musulumci ya nuna mana mahimmancin yin bincike idan an zo neman aure. Shi ne za ka ga ana cewa wane ko wance kakansa ya taba hauka, amma a iya fahimta ta abin da ke faruwa ‘yanzu na kisan mazajen aure da mata ke yi, yawanci rashin adalcin maza ne da kuma rashin kunyar da ta yi wa mata katutu, wanda a ganinsu hakan ne wayewa. Don haka idan maza za su zamo masu adalci, mata kuma su zamo masu yi wa mazajensu biyayya za a samu saukin lamarin.” 

 

 

Bai da wani muhimmanci – Husna Muhammad Lawal

Daga Zainab Mukhtar

Husna Muhammad Lawal: “Gaskiya a ganina wannan sabon al’amari da ake so a fito da shi na duba kwakwalwa kafin a yi aure ba abu ne mai muhimmanci ba, domin kuwa ciwon hauka ko matsalar kwakwalwa zai iya kama mutum ne a kowane lokaci ba kamar sauran gwaje gwaje da ake yi kafin a yi aure ba. Kuma a ganina idan mutum yana so ayi mishi gwaji, ba sai zaiyi aure ba. Don haka ina gani duk salon neman magana ne da ba shi da muhimmanci.”

 

 

Yin gwajin shi ya fi dacewa – Ummullazina Hassan

Ahmed Garba Mohammed, Kaduna

Ummullazina Hassan: “Gaskiya ina goyon bayan a rika yi wa ma’aurata gwajin kwakwalwa kafin su yi aure.  Yin haka zai sa a rika gano wadanda ke da matsala kuma a yi saurin magance ta kafin su yi auren.  Idan aka yi la’akari da yadda ake yawan samun tashin hankali a tsakanin ma’aurata ta hanyar kashe juna ko raunata juna, abin akwai daure kai.  Ta yaya za a ce an yi auren soyayya, amma abin ya kare da bakin ciki ta hanyar kashe juna?  Wannan wani abu ne da ya kamata a gudanar da bincike a kai, kuma daya daga cikin hanyoyin da za a bi don a kawo karshen wannan matsala ita ce ta yin gwajin kwakwalwa.”

 

 

Ya kamata a rika gwada wa -Haruna Lawal Sa’idu

Daga Zainab Mukhtar

Haruna Lawal Sa’idu: “Ya kamata a rika gwajin kwakwalwa kafin a yi aure saboda kada mutane biyu da ba su da ganewa da fahimta su auri junansu. Hakan zai taimaka wajen rage haihuwar yara da ba su da ganewa tun da masana rayuwar dan Adam sun yi bincike sun gano cewa su yara suna gadon basira da fahimta a wajen iyayensu musamman ma mahaifiyarsu. 

 

 

A rika gwada kwakwalwa kafin a yi aure – Zainab Yusuf

Ahmed Garba Mohammed, Kaduna

Zainab Yusuf (Zee ’Yar Mamanta): “A ra’ayina game da wannan batu na amince dari bisa dari a rika gwada kwakwalwar ma’aurata kafin su yi aure.  Ina nufin  ma’auratan biyu wato miji da mata.   Dalilin fadin haka kuwa shi ne bai kamata a rika yin boye-boye a cikin lamarin aure ba.  Za ta iya yiwuwa daya daga ciki ko duka su biyun suna da wata matsala da ta shafi kwakwalwa, amma tun da ba a yi gwaji ba, ba za a taba ganewa ba, sai wani abu ya faru daga baya sai a koma ana ’yan kame-kame.

“An sha samun labarai marasa dadi game da ma’aurata inda za ka tarar wata ta kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka ko kwalba ko zuba masa ruwan zafi ko ta hanyar zuba masa guba a cikin abinci, da sauransu.  Kamar yadda ake samun labarin yadda miji yake kashe matarsa ta hanyar datsa ta da adda ko soka mata wuka ko shake ta da sauransu.

Ga masu aikata irin wadannan halaye akwai nau’in tabin hankali da ke bukatar a gudanar da binciken kwakwaf kafin a gano.  Don haka na goyi bayan a rika yin gwaje-gwajen kwakwalwa ga duk ma’aurata kafin a amince su yi aure.”