Ya dace a rika gwada kwakwalwar shugabanni kafin su fara mulki?

A kwanakin baya ne Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci a rika yi wa shugabanni gwajin miyagun kwayoyi. Wannan furucin na sarkin Kano ya haifar da cece-kuce tsakanin al’ummar kasa baki daya. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin tab akin mutane, kuma ga amsoshinsu:   Gwada Qwakwalwar ba shi ne […]

Ya dace a rika gwada kwakwalwar shugabanni kafin su fara mulki?

A kwanakin baya ne Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci a rika yi wa shugabanni gwajin miyagun kwayoyi. Wannan furucin na sarkin Kano ya haifar da cece-kuce tsakanin al’ummar kasa baki daya. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin tab akin mutane, kuma ga amsoshinsu:

 

Gwada Qwakwalwar ba shi ne mafita ba – Muhammadu Sabiu

Isiyaku Muhammed

Muhammadu Sabiu: “Me ya kawo zancen haka? Ina kyautata zaton ba komai ne ya kawo wannan batu ba illa neman ’yanci da walwalar talaka a kasashe irin su Najeriya – kasar da har yanzu tasowa take yi.

Idan ka duba kasashen Turai, Amurka da Asiya, za ka fahimci cewa akwai shugabannin kasashe da firaminista-firaminista da suke gudanar da dabi’unsu ta yadda idan mutumin Najeriya ya kalle su, zai dauka ba su da hankali. Alal misali, idan mutum – musamman dan Najeriya – zai nutsu ya kalli kalamai da ayyuka irin na shugaban Amurka, Donald Trump, zai fahimci cewa shugaban na da bukatar shi ma ayi masa gwajn kwakwalwa. Ha ka ma, idan ka duba kasashe irin su Philippines, haka abin yake. Akwai wata rana da tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya je wani taro kasar. A yayin haka, sai shugaban Philippines, Rodrigo Duterte, ya zage shi da mummunar kalma, wato ya kira shi da “dan karuwa”. To ka ga wannan ma wani al’amari ne da ke bukatar sai an hada da likitoci.

“Ka ga ke nan gwajin kwakwalwa wa shugabanni kafin su fara mulki ba shi ne mafita ba – abin sa’a ne da kuma wasu dalilai da ban kirgosu a nan ba. 

“Daga karshe, Idan ya zamana kafin shugaba ya hau mulki sai an gwada kwakwalwarsa, to hakan zai kawo sabon al’amari wanda watakila ya jefa alu’umma cikin wani bala’in da ya fi na yanzu muni. A yayin gwajin kwakwalwa, ana iya rashin sa’a a cikin masu nagarta da za su iya tafiyar da mulki, sai su samu cikas saboda wata ‘yar matasalar kwakwalwa da ba-ta-kai-ta-kawo ba. Daga nan sai a ce ba su cancanta su yi mulki ba. Maimakon haka, sai ka ga an yi rashin sa’a an zabo wanda mugun nufi gare shi. Ka ga ke nan gwajin kwakwalwa bai haifar da da mai ido ba.”

 

Gwajin kwakwalwar ya dace – Fadila Sani

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Hajiya Fadila Sani: “Yana da kyau a rika yi wa shugabani gwajin gwagwalwa saboda kar mutum ya zama shugaba a dauka mai hankali ne, amma yana aikata abubuwa na marasa hankali. Annabi Muhammad SAW ya ce akwai lokacin da zai zo jahilai su zama shugabanni sannan kuma bakauye ma zai mulki ‘yan birni. Al’umma ya kamata su hankalta wajen zaban wanda zai zama shugaba don kar mutum ya zo da babbar riga basu tabbatar da lafiyar sa ba su zabeshi basu san bai da cikar kamala ba.”

 

Ya kamata a rika gwada kwakwalwarsu – Alfred Chidi

Daga Ahmed Ali, a Kafanchan

Alfred Chidi: “Xari bisa dari ya dace a rika yiwa shugabanni ko masu neman mulki gwajin kwakwalwa kafin amsar ragamar mulki a kasar nan saboda hakan shi zai taimaka wajen rage matsaloli da yawa da ke damunmu a kasar nan. Ko ba komai hakan zai taimaka musu su ma don sanin hakikanin wane hali su ke ciki su ma na shin ya dace su shugabanci mutane ko ko su koma su nemi lafiyar kwakwalwarsu. Yin hakan ina ganin ba tozarci bane domin shi zai taimaki kasar mu. Ai ina jin babu wani mutum a doron duniya da zai ce shi kwata-kwata bai da wata damuwa. Al’amarin wasu shugabannin kasar nan akwai matukar daure kai da ban tsoro domin yadda Allah ya albarkace mu a kasar nan da a ce muna sa’an shugabanni da lamarinmu ya bunkasa fiye da yadda ake zato.”

 

Zai iya amfani – Yunus Bello

Yunus Bello: “A tunanina gwada kwakwalwar shugabanni zai iya yin amfani, amma kuma zai iya haifar da wata matsala daban. Amfaninsa kawai shi ne a gano ko mutum na da tabin hankali, amma kuma sau da yawa za ka mutum na da tabin hankali, amma shi ma bai sani ba. Sai na gwada a gano cewa bai da hankalin, duk da cewa ba mamaki shi mutumin kirki ne. akwai wasu kuma suna da hankalin, amma mutanen banza ne.”

 

Gwajin  zai  taimaka – Fatima Shuwa

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Fatima Ahmad Shuwa: “Gaskiya batun a fara gwajin kwakwalwar shugabanni kafin su fara mulki ya yi dai dai saboda hakan zai taimaka a san lafiyar kwakwalwar su. Lafiyar kwakwalwa ita ce lafiyar jiki, don idan shugaba bai da lafiyayyar kwakwalwa a wani lokacin idan tsananin aiki ya yi yawa, zai iya sa ka ga shugaba ya fitar da dokar da ba za ta yi wa magoya bayansa dadi ba. Idan aka fara gwajin kwakwalwar zai taimaka saboda hakan zai sa a gane cikakkiyar lafiyar shugaba wanda duk abin da ya taso ba a tunanin zai kasance a jerin wadanda basu da nagartar lafiya.

 

Ya dace a  gwada kafin su fara mulki – Yahaya Usman Rahama

Daga Ahmed Ali, a Kafanchan

Yahaya Usman Rahama: “Qwarai kuwa ya dace a rika yiwa shugabanni gwajin kwakwalwarsu kafin hukumar zabe ta ba su damar tsayawa takara ba ma sai an kammala zabe kafin amsar ragamar mulki ba. Abinda ya san a fadi haka kuwa sau da yawa za ka ga abinda masu neman mulkin nan ke fada yayin kamfen da neman kuri’ar jama’a idan sun dare karagar mulki sai ka ga kwata-kwata sun yi hannun riga da abinda suke fada maimakon hakan, sai ka ga sun koma wani abu dabam da ba shi cikin tsari. Wasu shugabannin idan ka kalli abinda su ke yi sai ka ga bai yi kama da na mai hankali ba don haka ni ina ganin ya dace a rika yin gwajin watakila komai zai dawo daidai kamar yadda ya kamata domin  wani lokaci in ka kalli halin wasu daga cikin shugabanni sai ka ga ko kare ba zai ci ba.”