Ya dace a rushe kananan Hukomomi a tsarin gwamnatin Najeriya?

A kwanakin baya ne kwamitin sauya yanayin tsarin Najeriya wanda Jam’iyyar APC ta kafa karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya gabatar da rahotonsa inda ya bukaci a rushe kananan Hukomomi a tsarin gwamnatin Najeriya. Wannan ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wannan bukatar, kuma ga amsoshin […]

Ya dace a rushe kananan Hukomomi a tsarin gwamnatin Najeriya?

A kwanakin baya ne kwamitin sauya yanayin tsarin Najeriya wanda Jam’iyyar APC ta kafa karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya gabatar da rahotonsa inda ya bukaci a rushe kananan Hukomomi a tsarin gwamnatin Najeriya. Wannan ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wannan bukatar, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Bai kamata ba – Abubakar Jibril

Daga Amina Abdullahi, Yola

Abubakar Jibril: “Bai kamata ba saboda kananan Hukumomi su na daya daga cikin wadanda ke kusa da jama’a musamman al’ummar karkara. Su na taka muhimmiyar rawa wajen ainihin kawo gwamnati kusa da su. Duk masifan da ya taso a kan talaka yake karewa don haka, manyan da ya kamata su gyara abubuwa. Don haka gaskiya ba kamata ba.”

 

 

Kada a rushe su – Abubakar Ustaz Ba matsala

Lubabatu I. Garba, a Kano

Abubakar Ustaz Ba matsala: “Ina ganin bai dace a rushe tsarin kananan Hukumomi ba saboda idan aka wayi gari babu kananan Hukumomi, to talaka ba shi da wata dama a wajen gwamnati, domin gwamnatin jiha ta yi masa nisa. Ta hanyar kananan Hukumomi ne talaka ke samun hanyar da yake kai kukansa a share masa hawaye. Don haka ina ganin a bar kananan Hukumomi  tare da ba su cikakkiyar dama yadda za su ci gashin kansu don  talaka ya ci gaba da amfana daga gare su.”

 

 

A gaskiya bai dace ba 

– Umar Usman   Daga Amina Abdullahi, Yola

 

Umar Usman: “A gaskiya bai dace ba domin idan an rusa akwai bangarorin da hakan zai taba mu talakawa tunda kananan Hukumomi sun fi kusa da talaka. Shugabannin kananan Hukumomin ne kawai ya kamata su gyara yadda suke aiki ta yadda talaka zai ji dadi. Amma rusawan bai da amfani.”

 

Ban goyi bayan haka ba – Malam Auwal

Isiyaku Muhammed

Auwal Aliyu Muhammed: “Gaskiya ban goyi bayan yin hakan ba. Muna matukar bukatar kananan Hukomomi a kasar nan. Ai a tsari irin na da, kananan Hukomomi sun fi muhimmanci, gwamnoni ne suka danne su shi ya sa ba sa aiki yadda ya dace. Kawai a ba su dama su yi aiki, kuma su ci gashin kansu. Idan aka yi haka kowa zai ji dadi. Amma rushe su ba alheri ba ne.”

 

Bai dace ba – Mansur Yaron Baba

Isiyaku Muhammed

Mansur Yaron Baba: ‘Gaskiya ban amince da wannan tsari ba. karamar Hukuma ce take kusa da mu a matsayinmu na talakawa kasancewar ‘yan majalisun jiha ba sa aiki yadda ya kamata. Ina tunanin kamata ma ya yi a kara musu karfi kuma a rika ba su kasafin kudinsu kai tsaye daga Gwamnatin Tarayya domin su yi aiki yadda ya kamata.”

 

 

A kyale 

su  – Abba Sulaiman Kiyawa

Lubabatu I. Garba, a Kano

Abba Sulaiman Kiyawa: “Gaskiya bai dace a rushe kananan Hukumomi a tsarin mulkin Najeriya ba domin su ne suke kusa da talaka. Ina ganin abin da za a yi shi ne a yi wasu gyare-gyare da za su sa su sami inganci wajen aiwatar da ayyukansu yadda talaka zai amfana. Idan aka ba kananan Hukomomi dama, za su sami damar yi wa mutane aiki sannan jama’a za su rika samun ayyukan yi cikin sauki.”