Ya dace a yi karin albashi a wannan lokaci da ake ciki na matsin tattalin arziki?
A makon da ya gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin na musamman da zai yi dubi a kan yiwuwar kara mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya. Kafa kwamitin ke da wuya, sai wadansu suka fara koke-koken cewa idan aka kara albashin, kayan masarufi ma za su kara tsada, koma mutane da yawa ba […]
A makon da ya gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin na musamman da zai yi dubi a kan yiwuwar kara mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya. Kafa kwamitin ke da wuya, sai wadansu suka fara koke-koken cewa idan aka kara albashin, kayan masarufi ma za su kara tsada, koma mutane da yawa ba sa yin aikin albashi. Wadansu kuma suke cewa ai dama tuntuni ya kamata a ce an yi wannan karin. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga amsoshinsu:
Ya zama wajibi a kara – Auwal Differences
Umar Muhammed Gombe
Auwal Adamu Differences: “Hakika ya dace, ko ma in ce ya zama wajibi akan gwamnati tayi hakan, ganin yadda farashin kayan abinci dana masarufi sukayi tashin gwauron zabo a kasuwanni. Sannan kuma ga mummunan talauci da kuma tsadar rayuwa da ta mamaye al’ummar kasarnan musamman ma’aikata masu neman abun sawa a bakin salati. Gaskiya ya dace a tausaya musu a kara.Bayan haka zanyi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatoci akan su kirkiro da sabbin tsare-tsare da zasu saukakawa al‘umma rayuwarsu ta yadda talakawa da ma’aikata zasu daina kwana da yunwa. Domin ko an karawa ma’aikata albashi idan har farashin abinci bai sauko ba, to da sauran rina a kaba. Don haka ni a ganina abubuwa biyu ya kamata gwamnati tayi idan har tana son kyautatawa ma’aikata, sune, karin albashi a sauke farashin kayan masarufi.”
Lallai ya kamata a kara – Adamu Attahiru
Umar Muhammed Gombe
Alhaji Adamu Attahiru: “Babu shakka tun lokaci mai tsawo a baya, ya kamata ace anyi karin albashi, kamin a shiga wannan halin na tabarbarewar tattalin arzikin da ya haddasa mummunar talauci a tsakanin al’ummarmu musamman ma nan Arewa. Saboda haka yanzu ne aka fi bukatar karin albashi ga ma’aikata, idan aka yi la’akari da lalurar da yake kan albashinsa ada, tayi tashin gwauron zabo zuwa ninki uku ko fiye da hakabisa yadda ya sabayi a baya, alhali shi kuma albashin nasa yana nan bai canja ba. Domin an wayi gari idan mai karbar albashin ya karbi kudinsa, bai ma san abinda zai yi da albashin ba, bai san ta ina zai soma don magance matsalolin kansa da na iyalansa ba. Don haka idan gwamnati ta yi wannan kari zai kawo canji kwarai da gaske.”
Bai dace a kara albashin ba –Muhammad Saleh Gandu
Lubabatu I. Garba, a Kano
Muhammad Saleh Gandu: “A gaskiya bai dace a kara albashi a wannan yanayi ba duba da irin abin da hakan zai haifar na tashin farashin kayayyaki. Kowa ya san yadda ake da zarar ‘yan kasuwa sun ga an yi karin sai su kuma su tayar da farashin kayayyaknsu. A ganina da a tsaya ana batun karin albashi kamata ya yi gwamnati ta samar da yanayin da za a samar da tsayayyen farashin kayyyaki ko kuma ta shigo cikin harkar kasuwanci , ma’ana ya zama ta samar da wuraren da za a rika sayar wa talakawa kayayyakin masarufi cikin sauki. Ina ganin wannan ya fi karn albashin da ake kokarin yi amfani ga talakawa. Gashi muna da matsala a kasar nan idan aka kra kudin kowane irin abu koda an sami sauki, to fa farashin ya zauna a haka ba zai sake saukowa ba.”
Ya kamata a kara wa ma’aikata albashi –Hauwa Iliyasu Garba
Daga Nasiru Bello a Sakkwato
Hauwa Iliyasu Garba: “Ya kamata a karawa ma’aikata albashi. Hujjata ita ce abubuwa sun yi yawa ga kudin makarantar yara, ga kudin abinci, ga kudin man abubuwan hawa idan kana da shi, idan ba ka da shi kuma, zirga-zirga zuwa wurin aiki da gida, kasan fa abubuwa yanzu duk sun canza, komai ba sauki. Don haka ma’aikaci na bukatar karin albashi don ya iya daukar kansa da iyalinsa, a daina ba shi da dama, a karbe da hagu. Gaskiya akwai ban tausayi yadda ma’aikata suke a kasar nan da rashin walwala.
Zai yi kyau idan aka kara albashi – Jamilu Shu’aibu
Lubabatu I. Garba, a Kano
Jamilu Shu’aibu: “karin albashi yana da amfani kwarai da gaske duba da halin da ake ciki game da yadda kayayyaki suka yi tashin gwaron zabi, kudin ma’aikaci ba ya isar sa ya iya gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum. Idan aka kara albashi sai kuma gwamnati ta zauna da ‘yan kasuwa domin samun mafita daga karin farashin kayayyaki, don ma’aikaci ya ji dadin ko ya amfana daga karin albashin da za a yi masa”.
Bai kamata ba idan gwamnati ba za ta iya kayyade farashin kaya ba – Hassan Muhammad Ladan
Daga Nasiru Bello a Sakkwato
Hassan Muhammad Ladan: “Idan har gwamnati ba za ta iya kayyade farashin kayan masarufi ba, to bai kamata ta kara albashi ba, domin a Najeriya mutum nawa ne ke aikin gwamnati? ko daya bisa uku na mutanen kasar nan bas u kai ba. Amma a gefen ma’aikatan duba da wahalar da suke ciki, suna bukatar a kara masu albashi ko za su samu saukin biyan kudin gida da sauran bukatun rayuwa, matukar gwamnati da gaske ta ke yi kan yaki da rashawa.
Idan har gwamnati na son ma’aikata su samu sauki, to ta sauko da farashin man fetur, wannan zai sa farashin kayan abinci da sauran kayan da ake bukata yau da kullum su sauko. Amma karin albashi ba tare da daukar wadansu matakai na rage farashi ba, za a yi kamar ba a yi ba.