Ya dace a yi sulhu da ‘yan Boko Haram?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa idan ’yan Boko Haram sun shirya za su ajiye makamai a shirye yake ya yi musu afuwa. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan ko ya dace a yi hakan, kuma ga amsoshin da suke bayarwa: […]

Ya dace a yi sulhu da ‘yan Boko Haram?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa idan ’yan Boko Haram sun shirya za su ajiye makamai a shirye yake ya yi musu afuwa. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan ko ya dace a yi hakan, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Ya dace a yi sulhu da su – Hussaina Idrees

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Hussaina Idrees, daliba, a nata ra’ayin game da batun ko ya dace gwamnati ta yi sulhu da ’yan Boko Haram, ta ce hakan ya dace.  Ta ce ai duk abin da aka ce za a yi sulhu a tsakani, ko fada mutum biyu suke yi aka yi sulhu, to, za a samu zaman lafiya mai dorewa to ina kuma a ce harka ce da ta shafi dukan al’ummar kasar nan musamman na Arewa?  Kamar karin maganar Hausawa ne da ke cewa “duk abin da hakuri bai ba ka ba, to rashin hakuri ma ba zai ba ka ba.” Matsalar kawai ita ce kada bayan an yi sulhun wadansu daga cikinsu su koma suna yakin sari-ka-noke, ma’ana su koma suna kai hare-hare ta bayan fage.

Don haka ina goyon baya 100 bisa 100 a yi sulhun, don shi zai samar da zaman lafiya da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.  Kashe-kashen sun yi yawa. An barnata dukiyoyin al’umma da Allah ne kadai Ya san adadinsu. 

 

Sulhu ne mafita ga rikicin Boko Haram – Kabiru Magaji

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Muhammad Kabiru Magaji: “Ra’ayina shi ne sulhu ne abin da ya kamata a yi da Boko Haram domin ko tashe-tashen hankali da ke faruwa a kasar Amurka na Alka’ida sulhu ne ya kawo karshensa. kasashen duniya ma na neman sulhu da ’yan ta’adda domin yaki ba abin da yake haifarwa sai asarar dukiyoyi da rayuka, kuma idan kasa kamar ta Amurka za ta nemi sulhu da ’yan ta’adda, me zai sa a Najeriya ba za a nemi sulhu da Boko Haram ba?

 

Maganar a yi sulhun bai taso ba – Salisu Kabuga

Umar Akilu Majeri, Dutse

Malam Salisu Kabuga: “Maganar a yi sulhu da ’yan Boko Haram da gwamnati bai taso ba lura da yadda aka kasa cimma matsaya a tsakanin kungiyoyin ISIS da Taliban a kasashen Gabas ta Tsakiya, amma da za a ce idan an yi sulhun za su rike alkawari, to sulhu abu ne da ya dace. 

Amma matsalar a nan ita ce idan ma an yi sulhun, za a iya samun wani bangare na kungiyar ya balle ya ce bai aminta da sulhun ba, saboda haka ni a ra’ayina maganar sulhu ma bai taso ba.”

 

Bai dace a yi sulhu da su ba – Hassan Idrees

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Hassan Idrees ya ce a gaskiya bai kamata a yi sulhu da su ba, a ci gaba da yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe su kawai domin ko an yi sulhun za su bi ta bayan fage ne suna ci gaba da kai munanan hare-hare.

Idan ban manta ba ai a shekarun baya akwai bangaren Boko Haram da aka yi sulhu da su amma har yanzu suna kai munanan hare-hare. Gaskiyar magana ita ce, idan gwamnati ta kuskura ta ce za ta yi sulhu da su, to kashin al’ummar kasar musamman wadanda ke zaune a yankin Arewa maso Gabas ya bushe, domin babu abin da sulhun zai tsinana sai ci gaba da kashe al’umma da wawure musu dukiya.  Kuma yanzu da gwamnati ta ci galabarsu ai ba sulhu aka yi da su ba, an nuna musu karfi ne, don haka a nawa ra’ayin a ci gaba da yakarsu kawai babu kakkautawa.

 

Ya dace ayi sulhu – Babangida Usman dan Maliki

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Babangida Usman Mai Atamfa danmalikin Progress FM Gombe: “Idan dai so ake a ci gaba da zaman lafiya to ya zama dole a rungumi hanyar sulhun nan domin ita ce hanyar da ta dace. Matukar sulhu zai kawo zaman lafiya don kauce wa tashe tashen hankula. Rashin zama kan teburi a yi sulhu ba zai haifar da da mai ido ba, domin a duk lokacin da ake cikin tashin hankali babu wani abu mai kyau da zai faru sai asarar rayuka. Duk duniya inda ake yaki, teburin sulhu ake hawa don shawo kan lamura a karshe.”

 

Akwai bukatar sulhu – Alhaji Suleiman Yusuf

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Suleiman Yusuf, Shugaban Jam’iyyar GPN ta Jihar Jigawa: “Akwai bukatar yin sulhun saboda shi yaki ba ya kawo ci gaba a kasa. Domin haka akwai bukatar a yi sulhu saboda rashin yin sulhu ba alheri ba ne ga duk kasashen da suke fama da matsalar rikici. Yin sulhun abu ne mai matukar kyau, matsalar kwaya daya ce, duk kasashen da ake yin rikici da kungiyoyi irin na Boko Haram sun kasa tsayawa a yi sulhu ba don komai ba sai kawai saboda son zuciya.”