Ya dace Buhari ya yi maganin matsalar karancin gurbin karatu – kungiyar NANS
kungiyar dalibai ta kasa wacce a takaice ake kira (NANS), ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo musu dauki wajen maganin kalubalen da daliban kasar nan suke fuskanta na karancin samun guraben karatu a manyan makarantun kasar nan.kungiyar ta yi kiran ne a wata takadar sanarwa da ta raba wa manema labarai […]
kungiyar dalibai ta kasa wacce a takaice ake kira (NANS), ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo musu dauki wajen maganin kalubalen da daliban kasar nan suke fuskanta na karancin samun guraben karatu a manyan makarantun kasar nan.
kungiyar ta yi kiran ne a wata takadar sanarwa da ta raba wa manema labarai ciki har da Aminiya wacce mataimakin shugaban kungiyar, Kwamared Ogunkuade Oluwatosin ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce karancin gurbin karatu a manyan makarantun kasar nan shi ne babban kalubalen da ke ci wa matasa tuwo a kwarya.
kungiyar ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa dalibai fiye da kashi 15 ne kawai suke samun gurbin karatu daga cikin dimbin dalibai masu yawa da suka cancanci a ba su gurbin da za su ci gaba da karatunsu.
Sanarwar ta nuna cewa rashin bai wa daliban damar ci gaba da karatun zai iya tilasta wa da yawa daga cikinsu shiga aikata laifuka da kuma ta’addanci.
kungiyar NANS ta ce wahalar da daliban suke fuskanta ya samo asali ne saboda karancin gurbin karatu a manyan makarantun kasar nan.
Sanarwar ta bayyana cewa irin matakan da manyan makarantun suke dauka wajen rage yawan daliban da suke dauka rashin adalci ne ga dimbin matasan da suka cancanci samun gurbin karatu a jami’o’i da manyan makarantun kasar nan.
Ta ce hakan ya janyo karuwar manyan makarantun bogi masu zaman kansu wadanda masu neman gurbin karatu ta kowane hali suke fadawa tarkonsu a duk shekara.
kungiyar ta yi takaicin yadda duk da yawan manyan makarantun da ake da su a kasar nan ba sa iya samar da gurbin karatu fiye da miliyan daya da dubu biyar a shekara.
Saboda haka sai kungiyar ta yi kira da shugaban kasa ya dauki matakan gaggawa na kara gurbin karatu ga dimbin matasa da ke neman ci gaba da karatu a manyan makarantun kasar nan.
kungiyar ta bukaci shugaban kasa ya sanya dokar ta-baci ga sashen ilimin kasar nan don a ganin kungiyar zai taimaka kwarai da gaske wajen tunkarar matsalolin da ke addabar bangaren.