Ya dace Gwamnati ta ci gaba da tsame hannunta daga sha’anin addini a Najeriya?
A tsarin mulkin Najeriya, gwamnati babu ruwanta da wani addini (Secularism), duk kuwa da cewa mafi yawa daga al’ummar kasar suna bin addinan Musulunci ne da na Kiristanci. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a ci gaba da zama a haka, ko kuwa a samu sabon tsari, yadda gwamnati za ta tsoma […]
A tsarin mulkin Najeriya, gwamnati babu ruwanta da wani addini (Secularism), duk kuwa da cewa mafi yawa daga al’ummar kasar suna bin addinan Musulunci ne da na Kiristanci. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a ci gaba da zama a haka, ko kuwa a samu sabon tsari, yadda gwamnati za ta tsoma hannu a ciki? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana na ra’ayoyin jama’a:
Ya kamata gwamnati ta koma tafarkin addini – Muhammad Hamisu
Adam Umar, a Abuja
Muhammad Hamisu Suleja: “Zai fi dacewa a dawo da tsarin gwamnati mai gudana a kan tafarkin addini a yankunan Arewa da ke da rinjayen mabiya addinin Musulunci. Inda kuma ke da rinjayen Kirista sai a tafiyar masu da gwamnatinsu a kan tsarin da ake kai a yanzu ko wanda suka zaba a matsayin na addininsu. Saboda manzon Allah (SAW) ya ce a duk lokacin da aka maida addini a baya to ba za a samu ci gaba ba, sannan ya ce za a samu ci gaba a inda aka sa shi a gaba. Ga kasar Saudiyya nan, ta isa misali.”
Tsarin addini a gwamnati ya fi dacewa – Muhammadu Lawaisu
Adam Umar, a Abuja
Muhammadu Lawaisu: “Tsarin gwamnati mai kula da addini shi ne zai kawo ci gaba fiye da kowane irin tsari. Kuma duk wata hidima da aka ce ba ruwanta da addini to babu adalci a cikinta. Wannan tsari da ake bi a yanzu, wanda aka gada ko aka kwaikwayo daga Turawa, tsari ne na zalunci na jari hujja wanda talaka bai da ta cewa a ciki sai mai karfin dukiya ko na mulki kawai.”
Rashin kula addini kuskure ne – Mu’awiya Abubakar
A. A. Masagala, a Benin
Mu’awiya A. Abubakar: “Ni dai a ganina da kuma abin da na fahimta dangane da batun cewa ko ya dace gwamnatin kasa ta dore a kan manufarta ta ba ruwanta da maganar addini, to kawai gaskiyar maganar ita ce wannan babban kuskure ne; wanda duk mai aiki da hankali da ilimi na hangen nesa ba zai taba cewa ya gamsu da irin wannan manufar a lullube ba. Dalilina kuma shi ne, domin idan muka yi amfani da hankalin da Allah Ya ba mu sai mu ga ce rashin sanya batun addini cikin tsarin mulkin kasar nan shi ne ya zama tushen bai wa wasu masu mummunar akida ta jahilci suka samu damar kafa kungiyoyin tada zaune tsaye cikin addini a kasar nan. Misali, irin Boko Haram da suke ci gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba. Kuma duk wannan yana cikin kasancewa tsarin ba ruwan gwamnati da addini. Don haka a gaskiya ya kamata gwamnati ta sanya batun addini a cikin tsarinta amma da sharadin ta dauki masu zurfin ilimin wadannan addinan biyu, ba masu hada husuma ko nuna son kai ba.”
Babu alheri gwamnati ta bar addini – Muhammad Bello
A. A. Masagala, a Benin
Muhammad Bello Sagir: “Ni a ra’ayina, ban ga wani wani abin alheri ba a ce wai ba ruwan gwamnati da batun addini a cikin tsarinta ba kuma kasa irin Najeriya, wadda akasarin al’ummarta duk mabiya addini ne. Don haka idan aka yi la’akari da rayuwar ’yan Najeriya a bangaren addini a yau sai a ga cewa maganar babu ruwan gwamnati da batun addini ba ta taso ba. Wannan yanayin tamkar kara zube da gwamnati ta ba kowa damar ya tafi ya je ya aiwatar da abin da ya ga dama ko barna ce bai dace ba.
“Domin da a ce gwamnatin kasar nan ta sanya batun addini a cikin shirinta na tsarin mulki, to lallai da masu mummunar akida a cikin shugabannin addinan nan ba za su samu damar cusa wa wasu mummunar akida irin tasu ta shedanci ba da ta saba wa koyarwar manzannin Allah. Don haka abu mafi a’ala shi ne, gwamnati ta sanya batun addini a cikin shirye-shiyenta na tsarin mulkin kasar nan. Yin hakan zai tsaftace shugabancinta kuma zai magance irin yawaitar matsaloli da ake cin karo da su a bangare na mabiya addinai a kasar nan.”
Bai dace gwamnati ta kyale addini ba – Sheikh Ibrahim
Hamza Aliyu, a Bauchi
Sheikh Ibrahim Hassan Jahun: “Tabbas ana cewa Najeriya kasa ce wadda babu ruwanta da addini, wannan magana kuskure ce, domin hakkin gwamnati ne ta kula da abubuwa guda uku na al’umma. Na farko dole ne ta kula da addinin mutane, sai kuma kare rayuka da dukiyoyinsu.
Saboda haka ina ba da shawara ga Gwamnatin Najeriya ta sa ido sosai game da harkokin addini kuma kowa ya san cewa mutanen kasar nan masu addini ne. Babu dalilin da za a rika cewa Najeriya kasa ce da babu ruwanta game da addini. Da yawa daga cikin ’yan Najeriya mutane ne masu kula da abubuwan da suka shafi addini kuma za mu ci gaba da ba da shawara ga gwamnatin kasar nan ta daina cewa babu ruwanta da addini, domin masu addinin ne suke zabe har mutum ya dare kujerar mulki.”
Ya zama dole gwamnati ta kula da addini – Rabaran dan Amarya
Hamza Aliyu, a Bauchi
Rabaran dan Amarya: “Abin da zan fada game da wannan batu shi ne, wajibi ne gwamnati ta sa bakinta game da addini, domin ’yan kasar masu addini ne. Akwai Musulmi akwai Kirista tun lokacin da Najeriya ta samu ’yancin kai, wadanda suke shugabannin kasar masu addini. To idan haka ne tabbas Najeriya kasa ce ta addini ba kamar yadda ake cewa babu ruwan kasar da addini ba. Bayan haka akwai abubuwa da dama na addini wadanda gwamnati ce ke sa ido a kai kuma ita take ba da umarni game da yadda za a tafiyar da su. Saboda haka a ra’ayina ina goyon bayan gwamnati ta ci gaba da tsoma bakinta game da harkokin addinai amma kada ta wuce makadi da rawa.”