Ya dace gwamnatin tarayya ta bada agajin kudi ga jihohi?
A kwanakin baya ne gwamnatocin jihohi suka shiga matsalar kudi, inda da yawa suka kasa biyan albashin ma’aikata, har sai da Gwamnatin Tarayya ta ceto su, inda ta tallafa musu da kudade na musaman. Abin tambaya a nan shi ne, wannan abu da Gwamnatin Tarayya ta yi, shin ko ya dace? Gwamnati ta yi daidai […]
A kwanakin baya ne gwamnatocin jihohi suka shiga matsalar kudi, inda da yawa suka kasa biyan albashin ma’aikata, har sai da Gwamnatin Tarayya ta ceto su, inda ta tallafa musu da kudade na musaman. Abin tambaya a nan shi ne, wannan abu da Gwamnatin Tarayya ta yi, shin ko ya dace?
Gwamnati ta yi daidai – Injiniya Ibrahim
John D. Wada
Injiniya Ibrahim Adamu: “Ni a nawa ra’ayin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daidai da ya taimaka wa wadannan jihohin nan da suka kasa biyan ma’aikatansu albashi. Domin idan ka lura, wasu daga cikin gwamnonin baya sun ci basussuka saboda haka wannan taimako da ya yi musu zai taimaka wa ma’aikata ya kuma ba su damar ci gaba da ba da gudunmowarsu a jihohinsu yadda ya kamata.”
Tallafin ya dace – Abubakar Adamu
John D. Wada
Alhaji Abubakar Adamu: “Ba shakka abin da Shugaba Buhari ya yi ya dace, domin kamar yadda ka sani shi shugaba ne adali. Dayake bai ji dadin matsalar da wadannan ma’aikata suka sami kansu ba, shi ya sa ya dauki wannan matakin taimaka musu. Kuma kiran da zan yi a nan shi ne, don Allah su kuma wadannan gwamnoni su ji tsoron Allah su biya ma’aikatan kudinsu. Kada su hana su hakkinsu. Domin idan sun hana su Allah zai tambaye su wata rana.”
Ma’aikata sun amfana – Babayo Modibbo
Hamza Aliyu,a Bauchi
Alhaji Babayo Modibbo: “Ina daya daga cikin ma’aikata a Bauchi. Tabbas watannin baya da suka wuce akwai jihohi da dama a Najeriya wadanda suka fuskanci matsalar rashin biyan ma’aikata albashinsu na watanni. Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ba da wasu makuden kudade ga jihohin da suka fuskanci matsalar rashin biyan ma’aikata albashinsu. Yanzu haka akwai jihohi da dama a Najeriya wadanda ma’aikata har sun fara walwala sakamakon yadda aka biya su hakkokinsu.
“Mun fatar gwamnonin da suka karbi kudaden za su yi adalci tun da gwamnati ta biya musu bukatu kuma da yawa daga ma’aikata sun amfana da kudaden. Idan ka duba sosai sama da kasha 85 cikin 100 na ma’aikatan Najeriya kullum suna fama da rashin albashi. Ina fatar Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da wannan tallafi ga ma’aikata domin ta haka ne za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Gwamnati ta kyauta – Alhaji Bala
Hamza Aliyu, a Bauchi
Alhaji Bala Abdullahi: “Kamar yadda kowa ya sani, a Najeriya muna da murhu guda uku a tsarin tafiyar da gwamnati. Akwai Gwamnatin Tarayya, ta jiha, sai kuma kananan hukumomi kuma dukkansu suna da amfani a wajen al’umma. Abin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na ba da umarni a ba da wasu makudan kudade ga jihohin da suke fama da talauci da rashin biyan ma’aikata albashi na watanni, a fahimtata ya yi daidai.
“Misali a jihata ta Bauchi akwai wasu sassa da idan an biya ma’aikata albashinsu za ka ga kowa yana walwala, domin sama da kasha 85 cikin 100 na mutanen Bauchi sun dogara da albashi ne. Kuma ya kamata al’umma su fahimci cewa ba ma’aikata zalla suke amfana da albashi ba, abu ne wanda ya shafi kowa da kowa. Kasuwanni da dama a Najeriya in an biya albashi za ka ga kowa yana dariya. Gwamnatin Tarayya ta kyauta sosai da ta ba da kudaden.”
Gwamnati ta yi rawar gani – Idris Ibrahim
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Idris Ibrahim Sulaiman: “Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi rawar gani wajen daukar matakin biyan wadannan kudade ga gwamnatocin jihohi domin biyan albashin ma’aikatansu na watanni da ya makale. Wannan ya dace kwarai da gaske saboda hakkin ma’aikatan ne da ya zama wajibi a biya su guminsu. Sai dai ina fata mai girma Shugaba Buhari da mukarrabansa masu rike amana za su sanya idanu sosai a kan wannan al’amari, domin tabbatar da ganin kudaden sun isa ga ainihin ma’aikatan da aka fitar da kudin dominsu.”
Tallafin ya zo kan lokaci – Musa Abdullahi
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Musa Abdullahi, “Hanzarta daukar matakin fitar da dimbin kudade daga asusun Gwamnatin Tarayya domin biyan ma’aikata albashi a jihohin kasar nan da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya yi daidai kuma ya zo ne a daidai lokacin da miliyoyin jama’ar Najeriya da duniya za su fahimci manufar wannan Shugaba ta damuwarsa ga halin kunci da rashin ci gaba da ake fama da shi a cikin kasar. Halin damuwa da ma’aikata suka samu kansu a ciki na tsawon watani 5 zuwa 6 ba su kadai ya shafa ba, domin ya haifar da wani sabon babi ne na kuncin rayuwa ga al’ummar kasar nan. Saboda haka ya kamata gwamnonin jihohi da aka damka masu wadannan kudade su tabbata sun biya hakkin ma’aikatan ba tare da karkatar da akalar kudin ga wasu ayyuka daban ba.”