Ya dace jama’a su rika saya wa ‘yan siyasa fom din tsayawa takara?

A cikin ’yan kwanakin nan, yanayin siyasar kasar nan ya dauki sabon salo bayan da wasu kungiyoyi suka saya wa  tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari fom din tsayawa takara. Kwatsam a wannan makon sai wasu kungiyoyin suka saya wa Gwamnonin jihohin Kano da Kaduna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da […]

Ya dace jama’a su rika saya wa ‘yan siyasa fom din tsayawa takara?
Ya dace jama’a su rika saya wa ‘yan siyasa fom din tsayawa takara?

A cikin ’yan kwanakin nan, yanayin siyasar kasar nan ya dauki sabon salo bayan da wasu kungiyoyi suka saya wa  tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari fom din tsayawa takara. Kwatsam a wannan makon sai wasu kungiyoyin suka saya wa Gwamnonin jihohin Kano da Kaduna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i. Wannan na ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyi mutane a kan ko ya dace a rika saya wa ’yan takara fom, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Gaskiya bai dace ba – Tasi’u danlami

Daga Adam Umar, Abuja

Tasi’u danlami: “A gaskiya ina ganin bai dace ba. Dalili shi ne su jagororin ne ya kamata su yi wa jama’arsu wata hidima ba talaka ya fitar da abin da ya kamata ya yi hidimar iyalinsa ba ya kashe a kan wani dan siyasa da sunan wai yana kaunarsa. Ban ga abin da hakan zai kara ba illa karfafa cin hanci da rashawa a harkar gwamnati, ta yadda idan dan siyasar da aka saya wa fom ya samu nasara zai ja wadanda suka saya masa fom din a jikinsa a matsayin su ne masu kaunarsa, sannan sauran al’umma kuma a dauke su na baya.”

 

Hakan zai kara gurbata siyasa – Ahmadu Shehu

Daga Abbas dalibi, Ile-ife

 Ahmadu  Shehu Salihu, Sarkin Samarin Ile-Ife: “A ra’ayina bai dace ba, saboda wannan kara gurbatar da tsarin dimokuradiyya ne a kasar nan. Kuma wannan yana nuni da cewa masu sha’awar shiga siyasa ake so a dakatar a hana musu kwarin gwiwar shiga a dama da su musanmman mata da matasa. Kuma dama ce da za ta bai wa tsarin nan na mulkin kama-karya da mulkin mallaka da ’yan siyasa suke yi mana inda suka mayar da mulki ya koma daga su sai ’ya’yansu da abokan yinsu. Don haka kamata ya yi Hukumar INEC ta dauki kwakkwaran mataki a kan wannan sabon salo.”

 

 Na goyi bayan a rika saya wa ’yan takara fom -Zainab Yusuf

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Zainab Yusuf (Zee ’Yar Mamanta): A ra’ayina ya dace al’umma su rika saya wa ’yan takara fom don su yi takara.  Hasali ma idan jama’a ne suka taru suka saya wa wani mutum fom don ya yi takara, to suna da damar su tuhume shi idan bai yi musu aiki ba. Kuma ai da wuya a samu mutumin da ya ci zabe a karkashin haka ya juya wa al’ummarsa baya, don tun farko mutumin kirki za a zabo, don haka da wuya ya ce ba zai yi aiki ba.  Kuma wani dalili shi ne zai rika ba wadanda suka cancanta amma ba su da kudi damar yin takara.”

 

 Ba laifi idan mutum ba ya kan kujera – Muttaka Mustafa

Daga Adam Umar, Abuja

Muttaka Mustafa Haruna: “Na goyi bayan hakan amma ba ga ’yan takarar da ke kan kujera ba. Jama’a su yi tunanin wani talaka da suka gamsu da yanayinsa sannan suka tabbatar zai iya amma kuma bai da kudin sayen fom din. A nan na goyi baya su yi karo-karon kudi su saya masa fom har ma da wasu hidimomi. Ina ganin rashin gaskiya ne mutum ya share shekara hudu yana mulki sannan ya ce ba ya da kudin sayen fom don tsayawa takara kamar yadda na ji an ruwaito wani Gwamna yana cewa. Yin haka tamkar yana boye dukiyarsa ce ga jama’a kuma alama ce ta rashin gaskiya.”  

 

Wannan kamar zuba hannun jari ne – Musa Baro Hadeja

Daga Abbas dalibi, Ile-ife 

Musa Baro Hadeja: “Alal hakika bai dace ba, domin idan mutum ya saya maka fom din neman takara kamar zuba hannun jari ne a gare shi, da kuma son juya akalarka wanda ka iya hana ruwa gudu. Wannan tamkar cin hanci ne ko rashawa ko toshiyar baki, domin duk wanda ka ga an saya wa fom don yana kan mulki ne. Ana yin haka ne domin toshiyar baki, don haka abu ne mara kyau  kuma hanya ce ta bude wa cin hanci da rashawa kofa, kuma hakan mayar da tsarin siyasar kasar nan siyasar kudi ce da mayar da siyasar ta zama daga wadanda suka harde a madafun iko sai ’ya’yansu,  shi kuma talaka ba a ba shi dama ba, dole sai in yana da ubangida. Ko talaka na da gudunmawar da zai bayar a siyasa an hana masa, domin su masu sayan fom din ba shela suke yi ba idan akwai talaka ya zo su saya masa, suna yi ne domin abin da za su samu. Don haka duk adalin shugaba ba zai yarda da wannan tsarin ba, domin hanya ce ta ba da toshiyar baki.”

 

Hakan ya yi daidai -Hannatu L. Ali

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Hannatu Labaran Ali mai rajin kare hakkin dan Adam: “A nawa ra’ayin na goyi baya dari bisa dari a rika saya wa ’yan takarar da suka cancanta fom din tsayawa kowace irin takara, musamman shugabannin da suke neman yin tazarce wadanda suka taka rawar gani.  Haka kuma a rika saya wa sababbin ’yan takarar da ba su da halin yin haka, wadanda ake ganin za su iya taka rawar gani idan suka samu iko.

Duk dan takarar da aka saya wa fom zai mayar da hankali wajen yin aiki, don ya sa idan bai yi ba, to zai gamu da fushin al’ummar da suka tsayar da shi.”