Ya dace Jonathan da Buhari su hakura da takara a 2015?

A kwanakin baya ne malamin addini, Dokta Ahmad Gumi ya ba Shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari shawarar cewa ya kamata su hakura da takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa a badi. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace su dauki wannan shawara ko kuwa? Ga abin da mutane daban-daban suke […]

Ya dace Jonathan da Buhari su hakura da takara a 2015?
Ya dace Jonathan da Buhari su hakura da takara a 2015?

A kwanakin baya ne malamin addini, Dokta Ahmad Gumi ya ba Shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari shawarar cewa ya kamata su hakura da takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa a badi. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace su dauki wannan shawara ko kuwa? Ga abin da mutane daban-daban suke cewa:

Ya dace su hakura da takarar – Malam Musa

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Malam Musa Damaturu: “A ganina, dangane da ra’ayin cewar ko ya dace Shugaban kasa Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari su hakura da takararsu, a gaskiya hakura da takararsu shi ne mafi a’ala ga al’ummar kasar nan. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, a gaskiya addini kan iya shigowa domin kuwa mutanen Kudu, wadanda akasarinsu Kiristoci ne da wuya su zabi Buhari. Haka nan mutane Arewa, wadanda akasarinsu Musulmai ne, da wuya su kuma su zabi Jonathan. Don haka akwai bukatar wadannan mutane biyu su hakura da takararsu, a zabo wadansu da suka cancanta daga dukkanin jam’iyyun nan biyu don su yi takara. Hakan shi zai kawo zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.”

Su hakura da takarar shi ya fi – Abubakar Buba

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Shugaba Abubakar Buba Wanzami: “A ganina, takaddamar da ake yi kan cewar wai Shugaban kasa Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari da su janye daga takararsu, a gaskiya akwai bukatar duba lamarin. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, in har Jonathan ya ce ba zai janye ba to kuwa shi ma Buhari bai dace da ya janye ba, domin kuwa Buhari shi ne kawai zai iya bugawa da Jonathan ba tare da tsoron komai ba. To amma in har dukkansu za su iya hakura su janye saboda zaman lafiyar kasa to da dai sun yi dattaku, kasancewar akwai yiwuwar batun addini da bambancin yanki su iya tasowa, matukar su biyun nan ne za su tsaya takarar neman shugancin kasa.”

Bai dace su hakura da takarar ba – Usman Umar

Adam Umar, Abuja

Usman Umar: “A gaskiya bai dace ba, kodayake yana da damar fadin ra’ayinsa a matsayinsa na dan Najeriya sai dai a kullum yana da kyau mutum ya yi taka-tsan-tsan wajen bayani a kan al’amura irin wadannan masu sarkakiya da kuma tasiri, musamman ma dai a irin halin da kasar nan take ciki a halin yanzu. Wanda ba ma jin za a shiga wani hali da ya wuce wanda ake ciki a yanzu.”

Shawarar ba ta dace ba – Saminu Sani

Adam Umar, Abuja

Saminu Sani Azare: “A siyasance bai dace ba, domin shi Dakta Ahmad Gumi an san shi ne amatsayin malamin addini wanda kima da dattakun mahaifinsa ya sa ake martaba shi kuma yana tare da tarin mabiya da mahaifinsa ya share tsawon lokaci kafin ya tara su, wadanda na tabbata da yawa daga cikinsu mabiya Buhari ne. Ashe ya fito ya nuna kyamarsa ga Buhari ba karamin rarrabuwar kai zai jawo a tsakaninsu ba, baya ga bakin jini.”

Bai kamata su hakura ba – Abdu Garba

Isa Muhammad Inuwa, a Kano

Abdu Garba Yakasai: “Da farko dai Ahmad Gumi ya yi amfani da ’yancinsa na fadar albarkacin baki ne amma kuma idan muka duba matsayinsa na malami, ba haka ya kamata ya yi ba. Ya kamata ya yi jan hankali ga jama’a kan cewa su zabi shugaba nagari kuma su guji zaben shugaba maras inganci. Na farko, kasar nan tana cikin garari. Na biyu kuma muna neman wanda zai cece ta, ya kawo gyaran da ake bukata kuma babu wanda ya fi dacewa da hakan a yanzu sai Janar Buhari. Buhari kuwa mutum ne da kowa ya shaidi ingancinsa da gaskiyarsa da amanarsa, wanda kuma irinsa ake bukata a wannan lokacin wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da rashawa da barnatar da dukiya da ake ciki a yanzu.
Shi kuwa Jonathan idan muka duba, za mu ga cewa ya gaza a mulkinsa da yake yi yanzu, wajen samar da dukkanin abubuwan da ake bukata.

Bai kamata su hakura ba – Abubakar Abdullahi

Isa Muhammad Inuwa, a Kano

Abubakar Abdullahi Aminu: “Na samu karanta wasu daga maganganun da malamin ya fada amma ni sai nake ganin a maimakon ya yi wannan maganar a kan Buhari, mutumin da kowa yake ganin girmansa da martabarsa a wannan kasar, kamata ya yi ya kawo gamsassun hujjoji da dalilai da za su gamsar da kowa cewa Buhari bai dace ba. Amma ni a ganina, ina ganin Buhari ya dace ya sake tsayawa takarar shugaban kasar nan, musamman ma a halin da kasar nan take ciki a yanzu. Idan kuma ba shi ne ya dace ba, to ai sai a fada mana wanda ya fi shi dacewa. Sannan kuma ni yadda na fahimci maganar tasa, tabbas da akwai siyasa a ciki, musamman ma da ya hada da Goodluck Jonathan cewa shi ma bai dace ya tsaya ba.