Ya dace Kwankwaso ya rika tura masu horarwa waje kamar yadda yake tura dalibai -Mustapa Umar Tallo
Mai horar da ’yan wasan kwallon kafa na “ Gwarzo Kwankwasiyya Babes”, Mustapha Umar Tallo ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da ya rika tura masu horar da ’yan wasa na kulob-kulob da ke jihar kasashen ketare don kara masu kwarewa kamar yadda yake tura dalibai zuwa kasashen duniya don […]
Mai horar da ’yan wasan kwallon kafa na “ Gwarzo Kwankwasiyya Babes”, Mustapha Umar Tallo ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da ya rika tura masu horar da ’yan wasa na kulob-kulob da ke jihar kasashen ketare don kara masu kwarewa kamar yadda yake tura dalibai zuwa kasashen duniya don karo ilimi.
Malam Mustapha Tallo Gwarzo yayi wannan kira ne a tattaunawar da ya yi da Aminiya dangane da kwazon da kungiyoyin kwallon kafa na kananan hukumomin Jihar Kano ke yi musamman a harkar gasannin da ake shiryawa lokaci zuwa lokaci.
Ya ce ko shakka babu Gwamna Kwankwaso yana kokari wajen karawa matasa kwarin gwiwa ta hanyar wasannin kwallon kafa, wanda a cewarsa hakan ya taimaka wajen hada kan matasa da sauran al’umma masu sha’awar wasan kwallon kafa a fadin jihar.
Tallo ya kara da cewa idan ana tura masu horar da ’yan wasa kasashen waje ko shakka babu za a sami kwararru wadanda za su kara fitar da jihar kunya a kowace irin gasa da aka shirya walau a cikin gida ko wasu sassa na duniya.
Malam Mustapha Umar Tallo ya kuma jaddada cewa gwamnan Jihar Kano ya kasance zakara ta fannin kyautata yanayin wasannin motsa jiki musamman kwallon kafa ta hanyar baiwa ’yan wasa da masu horar da su kyaututtuka masu karfafa gwuiwa.
Ya yi amfani da wannan dama wajen yin tuni ga Gwamna Kwankwaso a bisa alkawarin da ya yi na tallafawa kungiyoyin kwallon kafa da aka zaba daga kananan hukumomomi wadanda har yanzu ba cika musu wannan alkawari ba.
A karshe, Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya yi kira ga matasan Jihar Kano su ci gaba da kasancewa masu bin doka da son zaman lafiya ta yadda zamantakewa za ta kara inganta sannan ya hori kungiyoyin kwallon kafa na jihar su kara zage damtse wajen ganin sun kasance zakaru a harkar kwallon kafa.