Ya dace mahaifina ya tafi Majalisar Dattawa – Yakubu Jang
Mai bai wa Gwamnan Jihar Filato shawara kan Ayyuka na Musamman Mista Yakubu Jang ya bayyana cewa mahaifinsa kuma Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang ya dace ya tafi Majalisar Dattawa domin ya ci gaba da kawo ayyukan ci gaba ga jihar. Mista Yakubu Jang ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen […]
Mai bai wa Gwamnan Jihar Filato shawara kan Ayyuka na Musamman Mista Yakubu Jang ya bayyana cewa mahaifinsa kuma Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang ya dace ya tafi Majalisar Dattawa domin ya ci gaba da kawo ayyukan ci gaba ga jihar.
Mista Yakubu Jang ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron matasa magoya bayan Jam’iyyar PDP da aka shirya a garin Bassa da ke karamar Hukumar Bassa da ke jihar.
Ya ce Gwamna Jang ya yi ayyuka da dama na raya kasa a karamar Hukumar Bassa da Jihar Filato baki daya kuma ya taimaki al’ummar jihar a bangarori daban-daban. “Idan Gwamna Jang ya tafi wannan majalisa zai yi wa Jihar Filato wakilci nagari, domin ya san mutane da dama a Najeriya wadanda zai iya zama da su a majalisar don ya kawo wa jihar nan ci gaba,” inji shi.
Ya ce don haka ne Gwamna Jang ya fito wannan takara ta kujerar Majalisar Dattawa ta Filato ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP. Ya roki al’ummar Bassa da al’ummar yankin Filato ta Arewa baki daya su fito su zabi mahaifinsa Gwamna Jang a wannan takara da yake yi ta kujerar Majalisar Dattawa.
Har ila yau ya yi kira ga al’ummar Bassa da Jihar Filato baki daya kan su zabi dan takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar PDP, Sanata GNS Pwajok.
Ya ce Sanata GNS Pwajok mutumin kirki ne wanda yake sauraron jama’a kuma mai aiki tukuru ne. Don haka idan aka zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar Filato zai kawo ci gaba mai yawa a jihar.