Ya dace Majalisar dinkin Duniya ta shigo cikin matsalar ta’addancin barayin shanu a Zamfara?

A kwanakin baya ne sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad ya bukaci Majalisar dinkin Duniya da ta shigo domin samar da maslaha a ci gaba da rikice-rikice da ta’addancin day a dabaibaye Jihar Zamfara. Wannan kira na sarkin Anka ya sa wasu na ganin cewa sarkin na nuni da cewa jami’an tsaro sun gaza ken an, […]

Ya dace Majalisar dinkin Duniya ta shigo cikin matsalar ta’addancin barayin shanu a Zamfara?

A kwanakin baya ne sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad ya bukaci Majalisar dinkin Duniya da ta shigo domin samar da maslaha a ci gaba da rikice-rikice da ta’addancin day a dabaibaye Jihar Zamfara. Wannan kira na sarkin Anka ya sa wasu na ganin cewa sarkin na nuni da cewa jami’an tsaro sun gaza ken an, yayin da wasu kuma suke ganin ai ya yi daidai. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan dacewar haka, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Shigowar ta abin da ya kamata ne kwarai da gaske – Kwamared Murtala ST

 

Nasiru Bello a Sakkwato 

 

Kwamared Murtala ST: “Shigowar su abin da ya kamata ne kwarai da gaske don lamarin ya yi kamari. Ka ji abin da Sarkin Anka ya fadi na mutanensa su kare kansu kuma sun shirya su sanarwa kungiyar Tarayyar Afirka wat A. U. Akwai bukatar su shigo don a samu maslaha kar abin ya kai irin na fitinar Boko Haram. Don haka su shigo cikin lamarin ko a gano bakin zaren warware lamarin don abubuwa sun yi muni a Zamfara, sai ka tafi babban garin jihar kowa ya watse daga yara kanana sai mata da tsofaffi da jami’an tsaro. Matasa sun gudu saboda wannan fitinar, an kassara jihar akwai bukatar hukumomin duniya su shigo ciki.”

 

 

 

Dole ne ta shigo tun da gwamnati ta kasa – Hajiya Amamatu Abubakar

 

Nasiru Bello a Sakkwato 

 

Hajiya Amamatu Abubakar: “Dole ne su shigo tun da gwamnati ta kasa. A ce wai akwai gwamnati a Zamfara amma a rika yi wa talakawa kisan gilla da sunan barayin shanu, idan sata ce kudirin mutanen me ya sa suke kashe wanda ba ya da ko kaza kuma su shiga gari su kashe kowa: su kashe matan da suke so da wadda za su yi wa fyade nan take da wadda za su tafi da ita, mata na shan wulakanci a hannun mutanen, bayan an mayar da su zawarawa ko marayu. Don haka Majalisar dinkin Duniya ta shigo ciki ta kawo agaji 100 bisa 100 ina goyon baya don kare mutane da muhalli tun da gwamnati ta kasa, kuma tana wasa da nauyin da Allah Ya dora mata.

 

 

 

Na goyi bayan ta shigo -Fatima Abdullahi

Ahmed Garba Mohammed

 

Fatima Abdullahi:  A nata ra’ayin ta ce ta goyi bayan Majalisar dinkin Duniya ta shigo cikin batun saboda yadda a kullum ake yawan kashe Fulani makiyaya ba su ji ba, ba su gani ba a Jihar Zamfara.  Ta ce hakan ya nuna gwamnatin jiha da ta tarayya ta gaza a fannin samar da ingantaccen tsaro a Jihar Zamfara don haka zai fi dacewa idan Majalisar dinkin Duniya ta shigo cikin batun don ganin an magance matsalar.  Kamar yadda Hausawa kan ce ne durkusawa wada ai ba gajiyawa ba ne.

 

 

Shigowar Majalisar dinkin Duniya matsalar ta ya dace – Tanko Isa

Daga Ahmed Ali, a Kafanchan

 

Adam Tanko Isah (Wali) : “Jihar Zamfara, jiha ce da ta dade tana fuskantar Matsalar rashin tsaro a Tarayyar Najeriya. Bincike ya nuna cewar Mahara sun kashe sama da mutum ‘1000 a Zamfara cikin shekara shida’. Wannan ba karamin koma baya bane ta fuskar tsaro da tattalin arzikin Jihar harma da ta kasa baki daya. 

Shigowar Majalisar dinkin Duniya cikin wannan rikita-rikita abu ne mai kyau, wanda hakan na nuni da cewar Najeriya ta gaza wajen kawo cikakken tsaro a tsakanin al’ummarta. A ra’ayina Majalisar dinkin Duniya ta so ta yi ma latti wajen kawo dauki a wannan jiha ta Zamfara mai dimbin tarihin matsalar tsaro (garkuwa da mutane, sa’annan rikicin Manoma da makiyaya).” 

 

 

A yi taka-tsantsan a kai – Kamal Abdulkadir

Daga Ahmed Ali,  a Kafanchan

 

Kamal Abdul kadir: “Duk da dai aikin samar da zaman lafiya yana wuyan kowa kuma duk wanda ya ce zai kawo maka dauki kan wata matsala abin a yaba ne sai dai matsalata guda daya ne wacce na ke jin tsoro. Ba komai bane shi ne yin taka tsantsan wajen karban turawan yamma da ‘yan korensu wajen ayyukan samar da zaman lafiya domin idan an lura ina ne suka taba shiga aka samu cikakken zaman lafiya a duniya? Duk inda suka shiga sai ka ga suna da wata bukata a wajen ko dai na diban kaso na wani arziki baya ga lalata tarbiyyar wadanda ta tarar a wajen amma idan ba haka ba ai abin farin ciki ne su shigo tunda mu mun kasa kawar da matsalar da kanmu.”

 

 

 

Gaskiya bai dace ta shigo ba -Zainab Yusuf

Ahmed Garba Mohammed

 

Zainab Yusuf (Zee ’Yar Mamanta) ta ce a game da ra’ayinta a wannan batu sam bai dace a ce sai Majalisar dinkin Duniya ta shigo kasar nan za a iya shawo kan matsalar satar shanu da ta kashe-kashe musamman a Jihar Zamfara ba. 

Ta ce idan za a tuna ai gwamnati ta yi kokari wajen shawo kan matsalar ’yan Boko Haram kuma Alhamdulillah yanzu an samu sauki tun da za a iya cewa an samu raguwar akalla kashi 85 daga cikin 100 na irin hare-haren da suke kai wa.  In kuwa haka ne sannu a hankali za ta shawo kan matsalar masu satar shanu a Jihar Zamfara.  Don haka ban goyi bayan Majalisar dinkin Duniya ta shigo don kawar da batagari masu satar shanu ba, yin haka tamkar gazawa ne a bangaren gwamnati.