Ya dace matasa su dogara da kansu – Jelani Aliyu
Malam Jelani Aliyu wani dan Najeriya ne da ya shahara wajen zana motoci a duniya. A wannan tattaunawar da Aminiya bayan da ya gabatar da wata kasida a ranar bikin yaye daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kwanakin baya, dan asalin Jihar Sakkwaton ya shawarci matasan kasar nan kan su rika amfani da baiwar […]
Malam Jelani Aliyu wani dan Najeriya ne da ya shahara wajen zana motoci a duniya. A wannan tattaunawar da Aminiya bayan da ya gabatar da wata kasida a ranar bikin yaye daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kwanakin baya, dan asalin Jihar Sakkwaton ya shawarci matasan kasar nan kan su rika amfani da baiwar da Allah Ya ba su, domin dogara da kansu tare da bunkasa tattalin arzikin kasar. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da kanka?
Sunana Jelani Aliyu, ni dan asalin Jihar Sakkwato ne, sai dai an haife ni a Jihar Kaduna a shekaran 1966. Ni ne da na biyar cikin ’ya’ya bakwai da mahaifina mai suna, Alhaji Aliyu Haidar da mahaifiyata mai suna, Hajiya Sharifiya Hauwa’u Aliyu. Na yi karatun firamare da sakandare duk a Jihar Sakkwato bayan na kammala saboda kyakykyawan sakomokon da na samu, sai na samu gurbin karo karatu a kasar Amurka a shekarar 1990. Har ila yau, na yi karatu ne a makarantar da ake kira (College for Creatibe Studies, United States) kuma na karanci fannin (Automobile Designing) wato shashin zanan motoci. Kuma na yi wannan karatun ne daga shekarar 1990 zuwa 1994. Na gama da sakomako mafi kyawu Allah Ya yi mini baiwa tare da bani basira da kuma kwazo wajen karatu, hakan ya sa babban kamfanin kera motoci da ke Amurka ya dauke ni haya don muyi aiki tare da su a cibiyarsu da ke Jihar Michigan. Hakan ya ba ni damar fitar da duk wata baiwa da Allah ya mini ta bangare zane-zane, inda na yi zane-zane tasiwirar motoci masu yawa.
Aminiya: Ko za ka yi mana bayani irin motocin da ka kera?
To kadan daga cikin motocin da Allah Ya ba ni ikon kera su sun hada da Opel Astra da Pontiac G6 da Cadillac da kuma Bricks. Har ila yau, na kara samun tabbacin nasara bayan na kera motar (Chebrolet bolt) a shekarar 2007, motar ita ce ta kawo sauyi a masa’antar kera motoci a Amurka. Kuma daga nan na ci gaba da kere-kere inda na samu damar kera motoci a shekarar 2014 da suka hada da sake kera motar “Chebrolet Camaro, GM’s I come Sport Car.”
Aminiya: Ya ya kake ji da irin wadanan nasarori?
A gaskiya wannan nasara da na samu ta yi matukar faranta mun rai tare da karfafa ni da kuma kara min kwazo domin na samu kyaututtukan giramamawa da yabo a ciki da wajen Najeriya kadan daga cikin lambar yabon da nasamu sun hada da lambar girma ta gwamnatin tarayyar Najeriya mai suna MFR, da lambar girma ta Jihar Sakkwato mai suna Merit Award, duk a shekarar 2012 a cikin shekarar 2007 na karbi lambar girmamawa a kasar Amurka mai suna Crain’s Detroit Business American Dreamers a shekarar 2008. Karbi kyautar GM Chairman’s Best of the Best Honors Award.
Aminiya: Wadanne kasashe ka taba ziyarta domin ba da gudumawa?
Na ziyarci kasashe da dama domin ba da gudunmawa ta a lokuta daban-daban kadan da cikin kasashen da nake tunawa sun hada da kasar Amurka da Canada da kuma kasar haihuwa ta Najeriya, inda na zama bako mai jawabi a kan taro wanda aka yi wa take da eNigerian Conference” taro ne da aka yi shekarar 2014 a garin Abuja Nageriya.
Aminiya: Yanzu kana zaune a ina na ne?
To a halin yanzu ina garin Michigan ne da ke Amurka tare da iyalai na cikin kwanciyar hankali da walwala.