Ya dace Musulmi da Kiristoci su rungumi sulhu – Paparoma
Paparoma Francis ya ce ya dace Musulmi da Kiristoci su rungumi sulhu kuma tataunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban abu ne mai matukar wuya, amma tana da muhimmancin gaske.Paparoma ya bayyana haka ne a ganawarsa da Musulmi da Kiristocin kasar Kenya a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.Da yake jawabi kan harin da masu ikirarin kishin […]
Paparoma Francis ya ce ya dace Musulmi da Kiristoci su rungumi sulhu kuma tataunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban abu ne mai matukar wuya, amma tana da muhimmancin gaske.
Paparoma ya bayyana haka ne a ganawarsa da Musulmi da Kiristocin kasar Kenya a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka.
Da yake jawabi kan harin da masu ikirarin kishin Musulunci suka kai a babban kantin nan na sayar da kayayyaki da ke Nairobi, Westgate a shekarar 2013 da kuma Jam’iar Garrisa, Paparoma Francis ya ce bai kamata mutane su rika yin amfani da sunan Allah domin su nuna kiyayya ga wasu mutane ba.
A bangare guda, Paparoma yana gudanar da taron addu’oi a Jami’ar Nairobi.
An tsaurara tsaro a Jami’ar, inda ’yan sanda da sojoji ke yin binciken kwakwaf kan mutanen da za su shiga wajen addu’o’in. Akalla ’yan sanda dubu10 ne za su yi sintiri lokacin ziyararsa.
Har ila yau, Paparoman zai kai ziyara kasashen Uganda da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda take fama da rikice-rikice tsakanin Musulmi da Kirista.