Ya dace mutanen Jos su bar wa yankin Bassa kujerar Majalisar Tarayya – Sale Bayare
Alhaji Sale Bayare tsohon sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya ce (Miyetti Allah) ta kasa, yanzu ya fito neman takarar da Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a karkashin Jam’iyyar DPP. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ya kamata a zakuda da kujerar zuwa yankin Bassa: Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar […]
Alhaji Sale Bayare tsohon sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya ce (Miyetti Allah) ta kasa, yanzu ya fito neman takarar da Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a karkashin Jam’iyyar DPP. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ya kamata a zakuda da kujerar zuwa yankin Bassa:
Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar fitowa takara?
Sale Bayare: To, na fara yunkurin fitowa takarar wannan kujera ne tun da aka dawo mulkin dimokuradiya a 1999. Allah Ya sa a wancan lokaci wani daga karamar Hukumar Bassa, mai suna Lumumba Dar Adeh aka zabe shi kan kujerar a karkashin Jam’iyyar PDP. Da ya gama a shekarar 2003 aka zabi wani daga karamar Hukumar Jos ta Arewa mai suna Alhaji Shehu Sale Hassan a karkashin Jam’iyyar ANPP. A shekarar 2007 aka sake zaben Alhaji Sama’ila Abdullahi shi ma daga karamar Hukumar Jos ta Arewa a karkashin Jam’iyyar ANPP, sai a shekarar 2011 aka zabi Alhaji Sulieman Yahaya Kwande shi ma daga karamar Hukumar Jos ta Arewa a karkashin Jam’iyyar DPP. Don haka muka ga cewa a wannan karo ya kamata mu al’ummar karamar Hukumar Bassa, mu fito mu roki al’ummar karamar Hukumar Jos ta Arewa, su yi mana adalci su ba mu wannan dama ta kujerar Majalisar Tarayya a wannan mazaba. Bayan haka al’ummomin kananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa da ke wannan mazaba da dama, sun zo sun same ni kan cewa ya kamata na fito wannan takara. Saboda suna ganin cewa na cancanci na fito takarar daga yankin Bassa. Don haka na amsa wannan kira na fito, don in gwada karbuwar da nake da ita a cikin al’umma. Wannan ne ya karfafa mini gwiwar fitowa takara.
Aminiya: Wadanne kudurori kake da su ga wannan mazaba idan ka samu nasara?
Sale Bayare: Na san abubuwa da dama a wannan mazaba kusan shekara 30 da suka gabata. Domin na fara siyasa a wannan mazaba tun a 1986 a lokacin da na jiye aikin jarida a kamfanin buga jaridun The Nigerian Standard na gwamnatin Jihar Filato. Na fito takarar shugabancin karamar Hukumar Bassa. Bayan haka na rike mukaman siyasa da dama, kamar Sakataren Tsare- Tsare da na Watsa Labarai na tsohuwar Jam’iyyar NRC reshen Jihar Filato. Kuma na rike Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP har zuwa Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Filato. Don haka na fahimci abubuwa da dama da suke damun al’ummar mazabar da jihar. Saboda haka nake ganin idan na samu nasarar lashe kujerar na tafi Abuja, in Allah Ya yarda irin abubuwan da ba ma samu a mazabar, saboda rashin gata za mu samu. Domin zan rika kama kafar Gwamnatin Tarayya da abokan arziki a Najeriya da kungiyoyin kasashen duniya da suke tallafa wa mutane don ganin an tallafa wa al’ummar wannan mazaba.
Kuma babbar matsalar nan ta kiyayya da rashin zaman lafiya da take damun al’ummar wannan mazaba, in Allah Ya yarda zan yi amfani da wannan kujera a yi dokokin da za su kawo zaman lafiya a mazabar da Jihar Filato da Najeriya baki daya. Saboda haka matsalolin da suke damun al’ummar wannan mazaba na san su.
Aminiya: Me ya sanya ka fito takara a Jam’iyyar DPP, maimakon PDP mai mulki ko babbar jam’iyyar adawa ta APC?
Sale Bayare: To, kamar yadda ka sani a da ni dan Jam’iyyar PDP ne, domin da ni aka kafa ta a 1998. Amma sai wannan ta jam’iyya ta PDP ta dawo ta zama idan ba kana da wani ubangida, ko uwa a gindin murhu ba yunwa za ta kashe ka. Kuma a wannan mazaba maganar jam’iyya ba ita ce take gabanmu ba. Al’ummar mazabar suna duba cancanta ne, domin ka ga wannan jam’iyya ta DPP a zaben da ya gabata babu wanda ya san ta. Amma a lokaci daya aka fitar da dan takarar wannan kujera a karkashinta kuma aka fito aka zabe ta. Wannan ya sa muke ganin kowa ya san wannan jam’iyya mai alamar abarba a wannan mazaba. Kuma wanda muka zaba a karkashin jam’iyyar ya bar ta ya koma wata daban, don haka muka fito takara a karkashinta.
Aminiya: Ganin jajircewa da sunan da ka yi a lokacin da kake Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa, ba ka ganin hakan zai iya kawo maka matsala a wannan takara?
Sale Bayare: Wato ni mutum ne mai lafazi daya, wanda ba ni da harshen damo a rayuwata kuma abin da na gada ke nan. Wannan jajircewa ba wani abu ne da na zaba wa kaina ba, na tashi na tsinci kaina a ciki. Yadda ka ga na jajirce a lokacin da nake rike da sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa wajen kare hakkin Fulani makiyaya, a lokacin na yi hakan ne saboda an ba ni amana ne na shugabancin al’ummar Fulani. Domin na dauka idan aka ba ka shugabanci ya kamata ka yi duk abin da ya kamata a matsayinka na shugaba wajen kare al’ummarka koda za ka rasa ranka ne, saboda amana ce aka ba ka. Saboda haka ban damu da gabar da wani zai yi da ni ba, a kan amanar shugabancin da aka ba ni. Zan tsaya na ga cewa na yi abin da ya kamata kan shugabancin da aka ba ni.
Aminiya: Wane sako ko kake da shi ga al’ummar wannan mazaba?
Sale Bayare: Ina rokon al’ummar wannan mazaba musamman na yankin Jos ta Arewa su duba yau shekara 12 ke nan al’ummar karamar Hukumar Bassa ba su samu damar samun wannan kujera ba. Saboda haka muna rokon su zakuda da ita yankin Bassa tare da mara wa al’ummar yankin Bassa baya a wannan karon ta hanyar zabar dan karamar hukumar a wannan kujera.