Ya dace rashin NYSC ya hana mutum aiki duk kwarewarsa?
A makon jiya ne ’yan Najeriya suka shiga mamaki bayan Ministar Kudi Kemi Adeosun ta yi murabus daga matsayinta sakamakon rahoton da ya nuna cewa takardar tsame ta daga yi wa kasa hidima (NYSC) da ke cikin abubuwan da ake bukata kafin mutum ya fara aiki a Najeriya ta jabu ce. Wannan lamarin ya sa […]
A makon jiya ne ’yan Najeriya suka shiga mamaki bayan Ministar Kudi Kemi Adeosun ta yi murabus daga matsayinta sakamakon rahoton da ya nuna cewa takardar tsame ta daga yi wa kasa hidima (NYSC) da ke cikin abubuwan da ake bukata kafin mutum ya fara aiki a Najeriya ta jabu ce. Wannan lamarin ya sa wadansu ke ganin cewa bai ma kamata yin hidimar kasa ya zama sharadi na daukar aiki ba? Domin haka ne muka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan ko ya kamata rashin hidimar kasa ya hana mutum aiki?
Bai kamata ba – Mamuda Mai Taki Kwadom
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Malam Mamuda Mai Taki Kwadom, Shugaban ’Yan Kasuwa na Kwadom da Kewaye: “Bai dace a kori ma’aikaci kan satifiket din NYSC ba, saboda idan ya san aiki zai iya ba da gagarumar gudunmawar da mai takardar shaidar ba lailai ya iya bayarwa ba. Don haka ya kamata gwamnatin Najeriya ta duba ta gane takardar NYSC daban sanin makamar aiki daban, domin a da can baya mai takardar shaidar firamare aji 7 ya fi wani wanda ya gama sakandare a yanzu sanin aiki.”
Bai dace ba – Fatima Mohammad Lawan
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Fatima Mohammad Lawan: “Gaskiya ni a nawa ra’ayin idan har mutum ya kware ya san makaman aikinsa, bai kamata a kore shi ba saboda rashin takardar shaidar satifiket na hidimar kasa wato NYSC. A kasar nan idan mutum ya gama jami’a shekarunsa suka wuce 30 ba ya yin hidimar kasa, domin ai ba karatun ne aka ce bai yi ba, NYSC ne saboda kasashen duniya ba sa yin NYSC sai Najeriya. Idan gyara da aiki tsakani da Allah ake bukata a Najeriya a bar maganar NYSC a yi maganar iya aiki idan mutum bai iya aiki ba ne sai a kore shi amma idan ya iya sai a bar shi.”
Bai kamata don mutum bai da takardar NYSC a hana shi aiki ba – Umar Sa’idu Jama’a
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Umar Sa’idu Jama’a: “Idan har an bincika kuma an tabbatar da sahihancin takardun mutum musamman na digiri to bai kamata a hana shi aiki ko kuma a ce za a kore shi daga aiki ba saboda kawai ba ya da takardar yi wa kasa hidima. A ganina yin NYSC din ba shi ne mafi a’ala ba, matukar mutum ya yi karatun kuma ya san abin da yake yi.
Ai akwai takardar da in mutum shekarunsa sun kai wani adadi a kan dauke wa mutum zuwa yi wa kasa hidima sai dai a ba shi takardar da za ta dauke masa wancan aikin wanda hakan ke nuni da cewa yin hidimar ba shi ne mafi muhimmanci ba. Idan ka dauki misalin Ministar Kudi mai murabus Kemi Adeosun ai an tabbatar ta yi karatun sannan an gwada ta an ga ta iya aiki to mene ne na tsangwamarta kuma? Ina ganin ci gaba da hakan zai sa wadansu su mayar da abin ya zama siyasa wanda kuma hakan ba zai taimaka wa kasar nan ba.”
Yin hakan bai dace ba sam – Alhaji Sulaiman Isah
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Sulaiman Isah: “A ra’ayina shi ne yin hakan kwata-kwata bai dace ba. Me zai sa duk kwarewar mutum a ce ba za a ba shi aiki ba ko kuma za a kore shi daga aiki don kawai ba ya da takardar NYSC ko takardar ba ingantacciya ba ce? To yaya za a yi da wadanda suke zuwa su biya kudi a rubuta musu sahihan takardun digiri da na NYSC wadanda su kuma sam ba abin da suka iya kuma ba su da wata kwarewa sai an dauke su aiki a wata ma’aikata ko an ba su wani mukami daidai da irin takardunsu amma a karshe s a ga ba abin da suka iya ko suka sani a kai.
Masu yi wa kasa hidima nawa ne ake turawa yanzu da za ka ga ko cikakken rubutu ko karatu ma ba su iya ba, amma dole a ba su shaidar ko don suna da uwa a gindin murhu ko kuma don sun yi aikin a zahiri amma ba don suna da wata kwarewa ta musamman kan wanda bai yi ba.
Ya kamata gwamnati ta sanya abubuwan da suka fi muhimmanci ne da za su amfani jama’a a ba abubuwa marasa muhimmanci ga kasa ba.”
Gaskiya bai dace ba – Ahmed Musa
Daga Jamilu Adamu
Ahmed Musa Ecos Hayin Ojo, Sabon Gari, Zariya: “Gaskiya bai dace a hana shi ba dalilina kuwa shi ne za ka ga mutum ya yi shekara da shekaru yana karatu kuma za ka ga ya yi matukar kwarewa a fanninsa, To ka ga a nan bai kamata a hana mutum aiki ba domin bai yi wa kasa hidima ba (NYSC), hakan bai dace ba.”
Ban goyi bayan hakan ba – Nafisa Usman
Daga Jamilu Adamu
Nafisa Usman Dogarawa Zariya: “Ban goyi bayan a hana mutum aiki ba domin bai yi wa kasa hidima ba. Bai kamata dalibi ya kammala karatu har na shekara hudu zuwa biyar ba, amma a hana shi aiki sakamakon bai da shaidar yi wa kasa hidima, duk da za ka ga wadansu da kwarewarsu. Daga karshe ina kira ga gwamnati ta soke aikin yi wa kasa hidima (NYSC) duk a huta.”