Ya dace sabuwar gwamnati ta yi bincike ko ta ja layi kawai?

Nan da 29 ga watan gobe sabuwar gwamnati za ta hau karagar mulki. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace idan ta hau ta yi binciki gwamnatin baya ko kuwa ta ja layi kawai daga inda ta amsa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ya dace ta […]

Ya dace sabuwar gwamnati ta yi bincike ko ta ja layi kawai?
Ya dace sabuwar gwamnati ta yi bincike ko ta ja layi kawai?

Nan da 29 ga watan gobe sabuwar gwamnati za ta hau karagar mulki. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace idan ta hau ta yi binciki gwamnatin baya ko kuwa ta ja layi kawai daga inda ta amsa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ya dace ta gudanar da bincike – Aliyu Muhammad

Abubakar Haruna, a Legas

Aliyu Muhammad: “Ya kamata sabuwar gwamnati ta yi bincike kan duk wata badakala da aka yi da dukiyoyin ’yan Najeriya, don dawo na da hakki a kudaden da aka sata, saboda haka duk dan Najeriya yana da hakki kan dukiyar kasarsa. Ka ga idan gwamnati ta ce ba za ta binciki kowa ba, to babu shakka ta sarayar da hakkin mutanenta kuma babu shakka Allah zai tambaye ta ranar gobe kiyama.”

Gudanar da bincike zai sa kowa ya shiga taitayinsa – Majid Salisu

Abubakar Haruna, a Legas

Majid Salisu: “Ina da ra’ayin cewa sabon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya gudanar da bincike don yin haka zai sanya jama’a kowa ya shiga taitayinsa, domin idan bai yi binciken ba kowa zai yi abin da ya ga dama su; rika satar kudadenmu suna kai wa waje. Kuma ni a ganina binciken zai zama darasi ga shugabannin da za su zo nan gaba da sauran ’yan Najeriya baki daya.”

Ya dace sabuwar gwamnati ta ja layi – Usman Nasiru

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Usman Nasiru kauran Namoda: “Ni a ra’ayina, ya dace gwannatin Buhari ta ja layi ne ba ta waiga baya ba, domin a halin da kasarmu ke ciki yanzu idan ba layi aka ja ba, to za a koma inda aka fito ne kawai. Idan Buhari zai yi bincike, kamar ya ce zai yi binciken abin da ya faru daga shekara biyar ko bakwai ko goma, to zai shafi da yawa daga cikin magoya bayansa. Don haka ya tsaya kawai ya gyara mana tsaro da cin hanci da rashawa da wutar lantarki da kuma samar wa matasa aikin yi.”

Bai kamata sabuwar gwamnati ta ja layi ba – Yahaya Sa’idu

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Yahaya Sa’idu: “Ra’ayina shi ne, bai kamata sabuwar gwamnati ta ja layi ba saboda idan ta ja layi zai zama ke nan kamar duk wadanda suka yi sata ko rub da ciki da dukiyar jama’a sun ci banza ke nan, amma kamar yadda Buhari ya ce zai ja layi, to ana nufin sai wadanda nasu ya tonu su kawai za a hukunta. Don haka kada a ja layi, a kama duk wanda aka samu da laifi komai dadewarsa, in dai adalci za a yi, ba sani ba sabo. Don idan ba haka ba za su ci gaba da satar har zuwa lokacin da za a rantsar da sabon Shugaban kasa.”

Ya yi bincike sama-sama – Ibrahim Musa

Lubabatu I. Garba, a Kano

Ibrahim Musa Muhammad: “A ganina, ya akmata a ce zababaen Shugaban kasa ya yi bincike ga irin tabargazar da aka yi a baya, wanda aka kama da laifi ya dawo da kudin al’umma; idan kuma bai dawo da su ba to ya kamata ya fuskanci hukunci, domin kayan gwamnati na duk ’yan Najeriya ne. Sai dai muna shawrtarsa da cewa idan zai yi binciken, ya yi shi kadan kada ya zurfafa, domin kada ya tsaya yin binciken ya bata lokacinsa a haka har shekaru hudun su kare bai gabatar da aikin da ke gabansa ba. Mutanen nan ba karamar barna suka yi a taskar kasar nan ba.”

Ya kamata a binciki kowa – Kabiru KB

Lubabatu I. Garba, a Kano

Kabiru K. B. Carwash: “Zai yi kyau zababben Shugaban kasa ya binciki kowa har da gwamnonin da ke kusa da shi. Mu mun san yawancin mutanen da ke kusa da Buhari suna da nasu guntun kashin, ciki kuwa har da gwamnan jihata. Ya kamata ya bincike su, kowa ya dawo da abin da ya sata. Misali, an yi badakalar mai amma shiru kake ji, muna nan muna zuba ido Janr Buhari ya binciko wadanda suka yi wannan aika-aikar. Duk abin da mutum yake yi ya rika tuna Allah, ya kuma san cewa duk dadewa akwai ranar da mutum zai shiga rami.”