Ya dace shekarun dan takara su zama matsala a zabensa?

A muhawararmu ta wannan makon za mu duba cewa, shin ko ya dace shekarun dan takara su zama matsala a zabensa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato: Ya dace a kula da yawan shekaru – Aminu Muhammad John D. Wada, a Lafiya Aminu Muhammad Laminu: “Batun ko ya dace […]

Ya dace shekarun dan takara su zama matsala a zabensa?
Ya dace shekarun dan takara su zama matsala a zabensa?

A muhawararmu ta wannan makon za mu duba cewa, shin ko ya dace shekarun dan takara su zama matsala a zabensa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato:

Ya dace a kula da yawan shekaru – Aminu Muhammad

John D. Wada, a Lafiya

Aminu Muhammad Laminu: “Batun ko ya dace a rika la’akari da shekarun dan takarar mukamin siyasa, a ganina hakan ya dace, don a kullum shi babba abin da yake tunani shi ne yadda zai samar wa al’ummarsa abubuwan ci gaba da za su inganta rayuwarsu. Amma shi matashi kamar yadda ka sani shi dai a koyaushe ta kansa da abin da za a samu a yanzu-yanzu ke zuciyarsa. Saboda haka idan ana so a samu shugabanci nagari, ba a kasar nan kawai ba; a duniya baki daya to ya zama dole a rika yin la’akari da yawan shekarun dan takara.”

A rika la’akari da shekaru – Malam Sani

John D. Wada, a Lafiya

Malam Sani Mai Salati: “A nawa ra’ayi dai, ya dace a rika yin la’akari da shekaru wajen kujerun Shugaba kasa da na gwamnoni da sauransu. Don idan ka lura, shi babba yana da fahimta fiye da matashi kuma kamar yadda ake cewa, abin da babba ya hango a zaune yaro ko ya hau icce ba zai iya gani ba. Saboda haka kamar yadda na fada, yana da kyau a rika la’akari da batun shekaru a shugabancin kasar nan domin zai taimaka sosai wajen samar wa al’umma shugabanci nagari.”

A rika duba shekarun dan takara – Sani Isyaku

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Sani Isyaku Gusau: “Ni dai a ra’ayine, lallai ya dace a rika la’akari da shekarun mutane wajen tsayawa takara, domin idan da ana la’akari da shekaru da wasu ko kusa ba za su matso ba, wasu daga cikinsu su ne suka kashe kasar kuma ba su so wasu su zo su ma su yi. Sun maida abin gado kuma cikin masu kananan shekaru akwai masu basira da sanin ya kamata, don haka kula da shekaru yanada matukar muhimmanci kuma cikin wadanda suke tsayawa takara wasu ba za su iya bambance maka tsakanin gishiri da suga ba koda sun dandana a bakinsu. Ka ga ke nan akwai matsala.”

Kula da shekarun shi ne daidai – Tukur Ibrahim

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Tukur Ibrahim Gusau: Ya kamata a rika la’akari da shekarun ’yan takara. Abin da ya sa na ce ya dace shi ne, idan ba shekaru za a rika lura da su ba, wadannan mutanen ba za su taba bari a sanya shuagabanni wadanda
suka dace ba, domin su a tunaninsu ba bu wanda ya sani ko ya iya kamarsu; don haka a kullun su ne dai kuma ba su san sun girma ba. Ga matasa sun kare katarun digirori har da digirgir amma a banza amma idan da za a yi la’akari da shekaru, to gaskiya za ta yi halinta, ma’ana za su gane cewa sun girma kuma ba zai yiwu ka yi zamaninka ka yi na wani ba.”

Bai dace a kayyade shekaru ba – Sani Guri

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Alhaji Sani Guri Zubairu: “A nawa ra’ayi, bai dace a kayyade yawan shekaru ga ’yan takarar mukamai ba. Kamata ya yi duk mutumin da ya mallaki hankalinsa komai karanci da yawan shekaru a kyale su nemi irin mukaman da suke so. Batun da wasu suke yi cewa bai kamata masu yawan shekaru su tsaya takarar mukamai ba, wannan bai dace ba ko kadan domin duk inda ka ga yawan shekaru, to a nan ne ake samun hankali da natsuwa da sanin ya kamata. Saboda haka, ya kamata masu karancin shekaru su yi koyi da na gaba da su ne domin da tsohuwar zuma ake magani.”

A rika tantance shekarun ’yan takara – Abubakar Kabir

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Abubakar Kabir: “A ra’ayina, kamata ya yi duk mutumin da ya ba shekaru 60 baya bai kamata a ba shi damar tsayawa takarar wani mukami ba. A matsayina na dalibi, malamai a makaranta suna yawan fada mana cewa, yara su ne manyan gobe. Saboda haka ina ganin ya kamata a sakar wa masu karancin shekaru mara domin a ga irin kamun ludayinsu a kan harkokin mulkin kasar nan. Kuma ganin yawancin masu yawan shekaru sun rike wasu mukamai a baya, ina ganin ya kamata su koma gefe daya su hakura su ba masu karancin shekaru dama da shawarwari.”