Ya dace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da rike mukamin ministan albarkatun man fetur?
A kwanakin baya ne aka shiga wata matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, duk da cewa an shawo matsalar yanzu. Amma wannan matsalar ta sa wasu ‘yan Najeriya suke ganin lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai zabi domin ya bas hi minsitan man fetur din domin a lura da bangaren yadda ya kamata. Wannan […]
A kwanakin baya ne aka shiga wata matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, duk da cewa an shawo matsalar yanzu. Amma wannan matsalar ta sa wasu ‘yan Najeriya suke ganin lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai zabi domin ya bas hi minsitan man fetur din domin a lura da bangaren yadda ya kamata. Wannan ne ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga amsohinsu:
Buhari ya ajiye mukamin Ministan fetur – Zainab Turaki
Ahmed Garba Mohammed, Kaduna
Zainab Turaki: “A gaskiya game da yadda al’amurran kasar nan ke tafiya musamman a bangaren man fetur, yakamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ajiye mukaminsa na Ministan fetur kuma ya gaggauta nada wani don hakan zai ba shi damar fuskantar shugabancin kasa ba tare da ya raba hankalinsa gida biyu ba. A ganina hada taura biyu a lokaci guda abu ne mai wahalar taunawa kamar yadda wata karin maganar Hausawa take nunawa.
Yadda al’amurra suka rincabe a bangaren man fetur, kamata ya yi a samu wani tsayayye wanda zai sanya ido don ganin an samu gyara a wannan sashe.
Idan aka duba za a ga a halin yanzu shugaba Buhari matsaloli sun yi masa yawa, don haka ba zai taba samun sauki wajen gudanar da shugabancin kasa sannan ya cigaba da rike mukamin Ministan Harkokin Man Fetur ba. Wannan shi ne ra’ayina.”
Ya ba wani ministan mai – Alhaji Mohammed Husseini
John Wada
Alhaji Mohammed Husseini: “Ni dai a nawa ra’ayi ya dace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa wani wannan mukamin na ministan man fetur. Don koda yake marasa gaskiya suna da yawa a kasar nan. Amma na tabbata akwai masu adalci da za su iya rike mukamin ba tare da an samu matsala ba. A gaskiya idan zai bai wa wani daban mukamin, hakan zai yi kyau. Don bai kamata a ce yana Shugaban kasa kuma ya rike ministan mai ba.”
Ya ci gaba da rikewa – Alhaji Bilya Doya Zauro
Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi
Alhaji Bilya Doya Zauro: “A nawa ra’ayi ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da rike ministan man fetur, saboda da ace ba shugaba Muhammadu Buhari ne ke rike da ministan man fetur ba, da badakalar kudin man fetur da ake samu ta yi yawa, kuma da bashi bane ministan man fetur ba yadda al’ummar Najeriya suka shiga matsalar man fetur a kwanannan da sai mun kai wata biyar muna fama da matsalar. Amma da yake shi ne ministan man fetur har an fara kawo karshen matsalar, amma da wani ne da dashi za a hada kai da yan’ kasuwa a cutar da al’ummar Najeriya saboda bukatar kansu, duk wanda zai mutu ya mutu ba ruwan su.”
Kada ya sauka a mukamin Ministan Fetur – Ya Chilla Mohammed
Ahmed Garba Mohammed, Kaduna
Ya Chilla Mohammed, daliba da yanzu haka take karatu a matakin jami’a a nata ra’ayin ta ce: “A ra’ayina ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da rike mukamin Ministan Fetur kada ya kuskura ya ce zai sauka. Dalilin fadin haka kuwa shi ne, a yanzu da yake rike da Ministan man fetur wasu suna yi masa zagon kasa ina kuma a ce ya yi murabus ya ba wani da ba a san kamun ludayinsa ba.
Babbar matsalar da ake fuskanta a bangaren man fetur shi ne na bata-gari da na marasa kishin kasa. Yanzu ’yan kasuwa nawa ke boye man fetur kuma suke sayar da shi a bayan fage don samun kazamar riba? In kuwa haka ne sauka daga mukamin Ministan fetur ga Buhari ba ita ce mafita ba, mafita ita ce mu ji tsoron Allah kuma mu gyara halayenmu. Sannan gwamnati ta hukunta masu hannu a wajen kawo mata zagon kasa musamman a bangaren man fetur don ya zama darasi ga saura.”
Bai dace Shugaban kasa ya rike minista ba – Hajiya Aishatu Mbaka
John Wada
Hajiya Aishatu Mbaka: “Ina ganin bai dace Shugaban kasa ya rike ministan man fetur ba. Ai shi mutum ne mai jinni, don haka aiki zai masa yawa. Ba zai iya kasancewa a waje biyu a lokaci daya ba. Saboda haka shawara da zan bayar ita ce shi da kansa ya nemi wani mai rikon amana wanda ya ga ya cancanta ya rike mukamin ministan mai din ya bashi. Bayan ya yi haka sai ya rika sa ido a harkokinsa yana bashi shawarwari a duk lokaci da bukatar haka ya taso.”
Bai kamata ba – Alhaji Hudu Aliyu
Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.
Alhaji Hudu Aliyu Zauro: “A nawa ra’ayi bai kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da rike ministan man fetur ba, saboda ayyuka sun yi masa yawa. Badakalar da ake yi a wannan ma’aikata ba zai sani ba, a kwanakin baya an samu wata badakalar kudi tsakanin minista a ma’ikatan albarkatun man fetur Ibe Kachikwu da Shugaban Hukumar NNPC Maikanti Baru. Wannan ya nuna cewa don babu ministan man fetur kusa da su shi ya sa haka ya faru. Amma in akwai ministan man komai ya faru zai kira su a zauna a gyara.”