Ya dace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rika sa baki a rikicin siyasar jihohi?

Kasancewar Jam’iyyar APC mai mulki tana fama rikice-rikicen cikin gida a jihohi da dama na kasar nan. Wasu suna ganin bai kamata Shugaban kasa ya sanya ido yana kallon ‘ya’yansa suna rikici da juna ba, wasu kuma suke ganin shirunsa daidai ne. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a […]

Ya dace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rika sa baki a rikicin siyasar jihohi?

Kasancewar Jam’iyyar APC mai mulki tana fama rikice-rikicen cikin gida a jihohi da dama na kasar nan. Wasu suna ganin bai kamata Shugaban kasa ya sanya ido yana kallon ‘ya’yansa suna rikici da juna ba, wasu kuma suke ganin shirunsa daidai ne. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wanan lamari, kuma ga amoshin da suke bayarwa:

Sanya bakin Shugaban kasa a siyasar jiha daidai ne – Hauwa Isyaku

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Hauwa Isyaku: “A gani na ya dace Shugaban kasa ya rika sa baki a harkokin siyasar jihohi, ba siyasa kadai ba kuma a kowanne abu ya sa baki dai dai ne. Siyasar ce ta ba shi dama ya zama Shugaban kasar Najeriya kuma a jam’iyyarsa duk wani rikici da ya faru yana da dama ya sulhunta kowa don dinke baraka da za ta haifar da rudani da koma baya. Ba katsalandan bane don Shugaban kasa ya sa baki wajen bada shawarwari da za su yi amfani domin ba yadda za a yi Shugaban kasa ya bada gurguwar shawara da za ta dakile ci gaban harkokin siyasa.”  

 

Ya dace shugaban kasa ya 

rika tsoma baki – Yahaya Ibrahim (Mai Waina)

Ahmed Garba Mohammed, Kaduna

Yahaya Ibrahim (Iya Mai Waina): A nasa ra’ayin ya ce:  “A gaskiya a matsayinsa na Shugaban kasa ya dace Baba Buhari ya rika tsoma bakinsa don a shawo kan rigingimun da ake yawan samu a jam’iyyun siyasun da ke fadin kasar nan musamman ma a Jam’iyyarsa ta APC.   Hasalima ba a jam’iyyarsa ta APC kadai ba, hatta jam’iyyun adawa zai iya tsoma baki don ya ga an samu daidaito don haka ne zai kawo ci gaba mai ma’ana a siyasar kasar nan. Yawan shirun da yake yi ne ta sa ake yawan samun matsala a siyasar da ake yi a wasu daga cikin Jihohin kasar nan.

 

Kada ya tsoma baki a rikicin jihohi – Ummullazina Hassan

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Ummullazina Hassan:  A nata ra’ayina ta nuna ba ta goyi bayan Shugaban kasa ya rika tsoma bakinsa a rikicin siyasar jihohi ba.  Ta ce ya rike girmansa kawai a matsayinsa na uban kasa, don idan ya ce zai rika tsoma baki watakila mutuncinsa zai iya zubewa a wajen wadansu.  Don haka ina goyon bayan kada ya tsoma baki a kowane irin rikicin siyasa da ke faruwa a jihohi, ya mayar da hankalinsa wajen gudanar da harkar mulki ne kawai.  Wannan shi ne ra’ayina.

 

Yin hakan ya dace – Alhaji Usman Adamu

Daga John D. Wada, Lafia

Alhaji Usman Adamu Doya-amsin: “A nawa ra’ayi ya dace Shugaban kasa Muhammadu Bahari ya rika sa baki a rikicin siyasa a jihohin kasar nan. Don kamar yadda ka sani shi shugaba shi ne da hakkin tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya, ba tare da nuna bambanci ba. Dole ya sa baki ko ba don ‘yan siyasa da ke rigimar ba, don talaka da rigimar ka iya shafa kamar yadda ake karin magana cewa idan giwa suna fada, ciyawa ke shan azaba. Saboda haka a ra’ayina ya dace matuka ya rika sa baki yana warware rigingimun don wannan ma aikinsa ne a matsayinsa na Shugaba kasa da ta kunshi jihohin. Nagode.” 

 

Yana da kyau – Alhaji Muhammed Mailafiya

Daga John D. Wada, Lafia

Alhaji Muhammed Mailafiya: “A gaskiya yana da kyau ya rika sa baki. Sai dai kada ya nuna bambanci a yayin da yake shiga tsakanin, ko da ana rikicin tsakanin dan jam’iyyarsa ne da wani dan jam’iyyar adawa daban. Domin ta haka ne kawai sa bakinsa a rikicin zai yi tasiri ko nasara. Amma idan ya kasance yana nuna son kai saboda jam’iyyarsa ko wani abu makamancin haka, kamar yadda wasu shugabannin kasar  nan da bazan ambaci sunayensu ba suka yi a baya, to ina mai tabbatar maka cewa ba zai iya warware matsala ko rikicin ba. Gaskiyar lamarin ke nan.”

 

Bai dace ya rika tsoma baki ba – Zainab Turaki

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Zainab Turaki: Ita kuwa a nata ra’ayin ta nuna sam bai kamata a ce shugaban kasa Baba Buhari ya rika tsoma baki a rikicin siyasar da ke faruwa a jihohi ba, don a matsayinsa na uban kasa idan yana tsoma baki wasu za su iya cewa ya nuna bambanci, musamman ga wadanda abin bai yi wa dadi ba, hakan zai sa su rika yin korafi. A ganina ya bar jihohi su sasanta kansu kawai ba tare da ya tsoma musu baki ba. 

 

Ya dace shugaban kasa ya rika sa baki a siyasar jihohi – El-nafaty

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

dalhatu A. El-Nafaty Bolari: “A nawa ra’ayin ya dace Shugaban kasa ya rika sa baki a duk wata harkar siyasar jihohi saboda dalilai na kawo gyara. Ai kowacce jiha a karkashinsa take, don haka yake da ikon sa baki wajen ganin yadda suke gudanar da siyasarsu, idan akwai gyara ma zai iya gyara musu ta hanyar basu shawarwari wanda za su amfani al’umma baki daya. Rashin sanya baki wajen tafiyar da harkokin wasu jihohi shi ya kawo ake yawan samun koma baya da kuma matsalolin da suka sha kan gwamnatocin jihar.”