Ya damfari abokinsa Naira dubu 40 da nufin zai samar masa mata a auren Hisba
A yayin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi nasarar gudanar da auren zawarawa da ’yan mata 1,111 a karo na hudu, wani matashi mai kimanin shekara 27 mai suna Rabi’u M. Ibrahim, fakewa ya yi da auren ya damfari abokinsa.Rabi’u na Unguwar Tukuntawa kuma ma’aikacin wani kamfani, ya damfari abokin aikinsa mai suna […]

A yayin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi nasarar gudanar da auren zawarawa da ’yan mata 1,111 a karo na hudu, wani matashi mai kimanin shekara 27 mai suna Rabi’u M. Ibrahim, fakewa ya yi da auren ya damfari abokinsa.
Rabi’u na Unguwar Tukuntawa kuma ma’aikacin wani kamfani, ya damfari abokin aikinsa mai suna Adamu Zakari na Unguwar Sabuwar Gandu a Kano.
Asirin Rabi’u ya tonu ne a makon jiya bayan Hisbah ta gudanar da daurin auren, amma Adamu ya ga an yi ban da shi.
Ana zargin Rabi’u ya shafe watanni yana tatikar Adamu kudi har jimillarsu ta kai Naira dubu 40.
An ce Rabi’u ya ja hankalin Adamu ne bayan ya nuna masa hoton wata budurwa mai suna Rashida, daga nan sai ya ci gaba da karbar kudi ta fakewa da dalilai daban-daban cewa yana yi masa kokarin tabbatuwar aure tsakaninsa da budurwar.
Rabi’u ya shaida wa Aminiya cewa yana da mace daya da da daya, kuma Adamu ne ya tuntube shi game da auren Hisbah, sai shi kuma ya ce masa yana da hanyar da zai sa ya samu auren. Ya ce “Ya zo ya same ni ya ce yana son aure, sai na ce ni yanzu gaskiya lokacin auren nan bai yi ba da ya dame ni sai na dauko wani hoto na ba shi, na ce masa wannan ta yi? Sai ya ce “Eh, ta yi.”
Ya ce hoton ya dade a wurinsa kuma na wata yarinya ce makwabciyarsu a Kaduna, kuma yana ji a yanzu an yi mata aure. Ya ce bayan da Adamu ya dame shi da maganar ne kuma ganin ya matsu da auren, sai ya yi ta kabar kudi a wurinsa, amma da aka yi auren na kwanan nan ya ga ba a yi da shi ba, shi ne ya kai kararsa ga Hisbah.
Rabi’u ya tabbatar da karbar kudin da suka kai Naira dubu 40 kuma ya nemi afuwar hukumar, inda ya ce a shirye yake ya biya Adamu kudinsa.Kudin da Rabi’u ya karba daga Adamu kamar yadda suke rubuce a takardar kara, sun hada da Naira 5,000 ta neman alfarma daga Kwamandan Hisbah da Naira 1,000 ta fom da Naira 5,500 ta gwajin jini da Naira 5,000 ta kudin mota zuwa Adamawa don neman tallafi daga Atiku Abubakar da Naira 7,000 ta kayan Sallah ga amarya da kudin dakon kayan amarya da kuma wasu Naira dari uku uku da ya rika karba a kullum a lokacin azumi wai na shan ruwa da suka kai Naira 8,000.
Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce hukumarsu ta sha fadakarwa a kafafen watsa labarai cewa ba su wakilta kowa ya karbi kudin wani mai son yin auren ba. Ya ce duk mai son auren ba sai ya bi ta hannun wani ba, kai tsaye zai je hukumar ta Hisbah. Ya ce za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban shari’a don a hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.
Sheikh Daurawa ya ce sun fara aurar da mata 100 ne a karkashin shirin, kuma suka yi na 150, sannan na mata dubu, yanzu kuma dubu da 111.
Ya ce nasarorin da suka samu sun hada da karbuwar shirin ga al’umma da gudunmawar da kamfanoni da masu kudi suke bayarwa, sannan gwamnati ta ci gaba da ba shirin goyon baya. Ya ce za su sake mika sunayen mabukata na gaba ga gwamnati, don sake yin shirin na gaba.