Ya datse kan wansa saboda rikici a tsakanin ’ya’yansu

Alkalin Kotun Majistare da ke Dutse a Jihar Jigawa, Majistare Sadam Habib ya ba da umarnin a tsare wani makiyayi mai suna Gambo Sa’idu da ake zargi da datse kan wansa saboda fadan ’ya’yansu. Alkalin kotun ya ce a tsare Gambo Sa’idu ne na tsawon mako biyu a gidan yari kafin ’yan sanda su kammala […]

Ya datse kan wansa saboda rikici a tsakanin ’ya’yansu

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar

Alkalin Kotun Majistare da ke Dutse a Jihar Jigawa, Majistare Sadam Habib ya ba da umarnin a tsare wani makiyayi mai suna Gambo Sa’idu da ake zargi da datse kan wansa saboda fadan ’ya’yansu.

Alkalin kotun ya ce a tsare Gambo Sa’idu ne na tsawon mako biyu a gidan yari kafin ’yan sanda su kammala bincike a kan wanda ake tuhumar.

Da yake amsa tambayoyi a gaban alkalin, wanda ake tuhumar wato Gambo Sa’idu mai kimanin shekara 22 bai yi musun aikata laifin da ake tuhumarsa ba, inda ya ce duk abin da ake fada a kansa game da kisan dan uwansa gaskiya ne.

Saboda haka ne ma kotun ta yi umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da ’yan sanda za su kammala bincike a kan laifin da ake zargin ya aikata wanda da shi ne kotun za ta yi amfani wajen zartar da hukunci.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan fitowarsa daga gaban alkali, Gambo Sa’idu ya ce asalin fadansa da wansa Haladu wata doguwar gaba ce wadda ’ya’yansu suka haddasa saboda fada da suka yi. Ya ce sakamakon haka ne marigayi Haladu ya dauki sanda ya buge shi a daji, shi kuma shi ne ya dauki adda ya sare masa kai wanda sakamakon haka ne ya rasu.

Ya ce kashe dan uwansa Haladu ya jefa shi cikin nadama saboda ya rasa dan uwa duk da cewa ba uwarsu daya ba, sannan yana nadama saboda yanzu haka mahaifinsu karfinsa ya kare wanda hakan ke nufin gida ya lalace kuma ga shi ’ya’yansu kanana ne kuma karfinsu bai kawo su taimaki mahaifinsa ba.

Saboda haka ya bukaci kotun ta yi masa sassauci a kan duk hukuncin da za ta yi masa, ya kuma roki kotun da ta yi masa afuwa a kan laifin da ya aikata saboda sai yanzu ne ya fahimci cewa ba ya da wanda ya fi dan uwansa a duk fadin duniya.