Ya dauki nauyin shirya wa mabukata 100 aure kyauta a Sakkwato
Wani dan kasuwa mai tallafa wa jama’a a Jihar Sakkwato, Alhaji Umarun Kwabbo A. A. ya dauki kudurin daukar nauyin yi wa mutane 100 aure a Jihar Sakkwato, domin tallafi ga marasa karfi da ke son yin aure amma ba su da hali. Ya bayyana kudurin ne Sakkwato, a yayin gudanar da walimar auren ’ya’yansa […]

Wani dan kasuwa mai tallafa wa jama’a a Jihar Sakkwato, Alhaji Umarun Kwabbo A. A. ya dauki kudurin daukar nauyin yi wa mutane 100 aure a Jihar Sakkwato, domin tallafi ga marasa karfi da ke son yin aure amma ba su da hali.
Ya bayyana kudurin ne Sakkwato, a yayin gudanar da walimar auren ’ya’yansa hudu da aka yi a cikin makon da ya gabata.
Ya ce “ba shakka akwai wasu mutane a cikinmu da ke son ganin sun yi aure ko ma sake komawa dakunan aurensu amma saboda rashin galihu, ba yadda za su yi. Sakamakon haka na ga ya dace in tallafa masu, don daukar nauyin duk abin da ake bukata dangane da yin auren nasu kyauta.
“Zan dauki nauyi na dukkan abin da ya dace a wajen tabbatar da hada aure da tarewa a gidan auren na ma’aurata guda 100 a tsakanin ango da amarya saboda Allah da neman falalarsa.”
Attajirin, wanda shi ne Jarman Sakkwato ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a taimaka wa gwamnati wajen dauke mata wani nauyi, don ganin an bayar da gudunmuwa a cikin al’umma.
“Hakika duk abin da Allah Yake yi wa bawanSa ya yi mani, ba abin da nake fata ga samu a yanzu da ya wuce rahama da gafarar Ubangiji Allah (swt), don haka zan taimaka da dukiya da nake da ita a yanzu tun ina da sauran karfi da iko ga masu bukata,” inji shi.
Tun da farko a jawabinsa, Shugaban Kwamitin shirya walimar, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ya nuna godiyarsa ga irin namijin kokarin da jama’a suka bayar wajen gudanar da bukukuwan aure a cikin nasara tare da fatan alheri.
Taron walimar ya hada malamai daga ciki da wajen Jihar Sakkwato, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, manyan ma’aikatan gwamnati da suka hada da Sheikh Aminu Daurawa, Dokta Mansur Sakkwato, Dokta Atiku Zawiyya Gusau da Malam Muhammad Maccido Sakkwato. An gabatar da nasihohi tare da tunatarwa dangane da muhimmancin aure, yin sadaka da kuma hadin kai tsakanin al’ummar Musulmi baki daya.