Ya dura wa ’yarsa guba don ya kashe ta
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama magidanci bisa zargin yunkurin kashe ’yarsa mai kimanin wata biyu da haihuwa ta hanyar shayar da ita guba. Bayanai sun ce a ranar Litinin din makon jiya ne magidancin mai suna Isma’ila Lawan da ke Unguwar Jakara a birnin Kano ya jika shinkafar bera a ludayi ya dura […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama magidanci bisa zargin yunkurin kashe ’yarsa mai kimanin wata biyu da haihuwa ta hanyar shayar da ita guba.
Bayanai sun ce a ranar Litinin din makon jiya ne magidancin mai suna Isma’ila Lawan da ke Unguwar Jakara a birnin Kano ya jika shinkafar bera a ludayi ya dura wa jaririyarsa mai suna Fatima Isma’il, lamarin da ya sa jaririyar fita daga hayyacinta aka garzaya da ita Asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Da yake bayyana dalilinsa na yin wannan aika-aika, mahaifin jaririyar ya ce, ya yi haka ne a kokarinsa na son rabuwa da matarsa wato mahaifiyar jaririyar.
A cewarsa tun farko ya auri matar tasa ne ba tare da sanin iyayensa ba, don haka ya yi yunkurin kashe ’yarsu don ya kawar da duk wata alaka ko nasaba tsakaninsa da matarsa.
Mahaifiyar jaririyar Malama Saratu Yusuf ta ce a lokacin da abin ya faru da misalin karfe 11:00 na dare ta zaga ban-daki tana fitowa sai ta iske maigidanta yana shayar da jaririyar
ruwan gubar inda ta kwace ta daga hannunsa tare da fitowa cikin hanzari ta kai kara ofishin ’yan sanda, daga bisani aka tafi da jaririyar asibiti don ceto rayuwarta.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an ceto jaririyar tana kuma samun sauki.
Majiya ya kara da cewa mahaifin jaririyar yana tsare a sashin binciken manyan laifuffuka kuma za a gurfanar da shi gaban kotu tunda ya riga ya amsa laifinsa.