Ya farke cikin matarsa don gano abin da za ta haifa

Wani magidanci a kasar Indiya ya farke cikin matarsa mai juna biyu domin ya ga abin da za ta haifa namiji ne ko mace. Mutumin mai suna Pannalal, ya shiga hannun ’yan sanda bayan faruwar lamarin a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin Indiya. Yadda giya ta kashe sama da mutum 100 a Indiya Suruka […]

Ya farke cikin matarsa don gano abin da za ta haifa

Matar da aka fake wa ciki a asibiti

Wani magidanci a kasar Indiya ya farke cikin matarsa mai juna biyu domin ya ga abin da za ta haifa namiji ne ko mace.

Mutumin mai suna Pannalal, ya shiga hannun ’yan sanda bayan faruwar lamarin a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin Indiya.

Jami’in ’yan sanda PravinSingh Chauhan ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa matar tana cikin mawuyacin hali sakamakon raunin da mijin ya yi mata.

Ya ce “Yanzu muna bincikar dalilin da ya sa mijin ya aikata wannan danyen aiki.”

Dangin matar sun ce mijin yana da ’ya’ya mata 5 don haka yake tsananin son ya haifi namiji.

Sun ce mijin ya farke cikin matar ce don ya tabbatar da ko tana dauke da namiji a wannan karo.

Gidan Talabijin na NDTV ya ruwaito cewa matar tana dauke da cikin wata bakwai ne lokacin da mijin ya farke ta.

Duk da yadda gwamnati take ta kokarin wayar da kan jama’a, har yanzu a Indiya an fi fifita samun ’ya’ya maza a kan mata.

Mafi yawan mutanen Indiya sun fi ganin ’ya’ya maza a matsayin jari inda suke kallon mata a matsayin nauyi da wahala.

A shekarar 2018 an fitar da rahoton daake bayyana cewa duk shekara ana rasa ’ya’ya mata miliyan biyu sakamakon zubar da cikinsu da ake yi a qasar Indiya.

Zaben cikin da ake so a haifa na ci gaba da kamari sakamakon rashin doka mai karfi da za ta shawo kan matsalar.

“Muna sane da zaven abin da za a haifa kuma lamarin yana matuqar karuwa,” inji wani jami’in gwamnati.

“Wannan alamari na kyamatar ’ya’ya mata ya shafi daukacin mutanen Indiya ne,” inji rahoton.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7