Ya farke masa ciki a kan budurwa
’Yan sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Salisu Muhammad bisa zarginsa da farke cikin wani matashi mai suna Nura Yahaya a kan neman wata budurwa.Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce yayan wanda aka farke wa cikin ne ya sanar da ofishin ’yan sandan Rijiyar Lemo cewa […]
’Yan sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Salisu Muhammad bisa zarginsa da farke cikin wani matashi mai suna Nura Yahaya a kan neman wata budurwa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce yayan wanda aka farke wa cikin ne ya sanar da ofishin ’yan sandan Rijiyar Lemo cewa Salisu Mohamamd ya daba wa kanensa Nura wuka a ciki ya farke shi. “A yanzu haka matashin yana kwance a asibiti bayan likitoci sun yi masa aiki,” inji Majiya.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kofar gidan su budurwar. “Saboda an samu sabani a tsakanin Nura da budurwarsa (wacce aka boye sunanta) sai ya yi mata waya ya zazzage ta, ita kuma sai ta ce idan ya isa ya zo kofar gidansu ya same ta yanzu, sai Nura ya tafi. Ashe bai sani ba tana tare da Salisu. Zuwan Nura kofar gidan ke da wuya sai suka shiga gaya wa junansu maganganun batanci har suka kai ga kokawa a tsakaninsu. Kuma a wannan hali ne Salisu ya zaro wuka ya daba wa Nura a
ciki, inda ya fadi cikin jini,” inji shi. Majiya ya ce sun kama Salisu tare da budurwar da kuma yayanta.