Ya fi so ya yi rayuwa irin ta dabbobi
Wani mutum dan asalin kasar Birtaniya ya ce ya fi kaunar ya koma rayuwa irin ta dabbobi, kamar yadda jaridar Daily Mirror ta ruwaito.Mutumin mai suna, Thomas Thwaites, ya kyautar da dukkan abin da ya mallaka domin ya koma daji ya ci gaba da rayuwa tare da dabbobi.Har ila yau domin ya saje da su, […]
Wani mutum dan asalin kasar Birtaniya ya ce ya fi kaunar ya koma rayuwa irin ta dabbobi, kamar yadda jaridar Daily Mirror ta ruwaito.
Mutumin mai suna, Thomas Thwaites, ya kyautar da dukkan abin da ya mallaka domin ya koma daji ya ci gaba da rayuwa tare da dabbobi.
Har ila yau domin ya saje da su, ya sa an kera masa kafafu da hannayen roba wadanda suka yi kama da na dabbobin. Bugu da kari, ya sa likitoci sun masa aiki a cikinsa domin ya dace da cin ciyawa da sauran nau’in abincinsu.
Mista Thomas ya ce yana wadannan dabi’un ne domin ya samu wani dan wutu daga matsayinsa na dan Adam.
“Babban burina shi ne na samu wutu daga kasancewa ta mutum mai koshin hankali. Na fi so na kaurace wa tunanin abubuwan da suka gabata da kawar da damuwar abin da ke gaba. Wannan shi ne abin da ya sa na shiga daji, ina rayuwata da dabbobi. Ba na so na dora wa kaina damuwa,” inji shi.