Ya gano amaryarsa namiji ne bayan kwana 12 da aurensu
Daga hotunan bikin aure, za ku ga cewa da gaske yana kama da mace. Muryarsa tana da laushi iri ta mata.
Wani matashi ɗan ƙasar Indonesiya ya kaɗu bayan ya gano cewa matar da ya aura kwana 12 namiji ne.
Kafafen yaɗa labarai na Indonesiya sun ce matashin ɗan shekara 26 da aka ambaci sunansa da AK kawai, a ƙarshe an sanar da ’yan sanda bayan gano cewa amaryar namiji ne.
- Sarautar Kano: Yadda ’yan siyasa ke gwara kan ’yan uwa
- Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai karo na 15
Angon ya haɗu da amaryar ce ta Intanet, inda suka yanke shawarar yin aure.
AK ya ce ya daɗa kamuwa da son ta lokacin da ya gan ta a karon farko, hakan ya sa ya samu ƙarfin gwiwar tambayar lokacin aurensu.
‘Budurwar’ ta bayyana sunanta da Adinda Kanza Azzahra kuma takan ɓoye fuskarta da mayafi ko hijabi. Saurayin yakan ɗauka kunya ke sa ta haka.
Adinda ta amsa buƙatarsa ta su yi aure amma ta ce ba ta son a yi rajistar aurensu saboda mahaifiyarta ta rasu kuma ta daɗe ba ta ga mahaifinta ba, don haka ba ta da dangi na kusa da za ta gayyata zuwa bikin.
A ƙarshe, masoyan biyu sun yanke shawarar yin biki na musamman da shugaban addini na ƙauyen Wangunjaya ya jagoranta. Kuma a gidan AK aka gudanar, bayan sanya sadaki a kan giram 5 kacal na zinare.
Sai dai bayan auren Adinda ta riƙa wasan ɓuya da angonta, ta ƙi cuɗanya da ’yan uwa da abokan arziki a ƙauyensu.
Bayan ƙorafi daga AK, danginsa sun yanke shawarar bincike a kan amaryar inda suka gano mahaifinta na nan a kusa.
Shi ne ya shaida musu cewa Adinda namiji ne, da jaridun Indonesiya ke kira ESH.
Iyalin AK sun shaida masa batun, kafin su sanar da ’yan sanda. ESH ya ce yana son samun kuɗine daga wajen wanda ya aura.
Wata majiya daga ’yan sanda ta ce, “Duk lokacin da ESH ta nemi kuɗi, takan samu.”
An gurfanar da wanda ake zargin da aikata lafin da ya saɓa wa Sashe na 378 na kundin laifuffuka da ka iya kai shi ga zaman gidan yari na tsawon shekara huɗu.
Shugaban Sashin Manyan Laifuffuka na ’Yan sandan Naringgul, ya shaida wa manema labarai cewa ESh na kama da mace, musamman idan ya yi kwalliya.
“Lokacin da ya yi kwalliya, yakan kasance kamar mace,” in ji Bripka Ridwan Taufik.
“Daga hotunan bikin aure, za ku ga cewa da gaske yana kama da mace. Muryarsa tana da laushi iri ta mata,” in ji shi.